Bayan shekaru 3, Gwamnan Borno ya bude titin Maiduguri - Gamboru Ngala bayan shekaru 3

Bayan shekaru 3, Gwamnan Borno ya bude titin Maiduguri - Gamboru Ngala bayan shekaru 3

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude babban titin da ya hada Maiduguri da Gamboru-Ngala
  • Wannan ya biyo bayan rufe titin shekaru uku da suka gabata sakamakon hare-haren yan Boko Haram
  • Gwamna Zulum ya mika godiyar al'ummarsa ga jami'an Sojojin Najeriya bisa kokarinsu

Borno - Shekaru uku bayan rufe titin Maiduguri-Dikwa-Mafa-Gamboru Ngala mai tsayin kilomita 137 sakamakon hare-haren Boko Haram, gwamnatin jihar Borno da Sojoji sun bude titin.

Gwamna Babagana Umara Zulum yayin bude titin ranar Juma'a ya jinjinawa Sojoji da yan sa kai bisa taimakon da suka bada wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, rahoton ChannelsTV.

Hakazalika ya yi kira ga direbobi su hada kai da jami'an tsaro wajen tabbatar da rayuwa da kasuwanci sun dawo hanyar.

An yi taron bude titin ne a Muna kuma Gwamnan ya hau titin har zuwa Dikwa domin tabbatar da cewa lallai an bude hanyar gaba daya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Borno ta bude titin iyakar Maiduguri–Dikwa–Gamboru/Ngala

Maiduguri - Gamboru Ngala bayan shekaru 3
Bayan shekaru 3, Gwamnan Borno ya bude titin Maiduguri - Gamboru Ngala bayan shekaru 3 Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Titin Maiduguri-Gamboru Ngala ya kasance wani hanya mai muhimmanci da ya hada Najeriya da Kamaru, Chai, da Nijar.

Shekaru uku da suka gabata, an rufe titin ne sakamkon yawaitan hare-hare kan garuruwan Dikwa, Mafa da Gamboru Ngala.

Mamban kungiyar NURTW, Goni Bura, ya bayyanawa manema labarai cewa bude hanyan zai taimakawa yan Najeriya da makwantanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel