Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Jihar Kano - Za'a shirya Fim na musamman kan labarin Hanifa Abubakar, 'yar shekara biyar da mai makaranta yayi garkuwa kuma ya kashe a jihar Kano.

Ana kyautata zaton za'a fara haska Fim din a watan nan, rahoton DailyTrust.

Furodusan Fim din, Ali Sa'id ya bayyana cewa babban dalilin da yasa ya shirya wannan Fim shine wayar da kan iyaye kan yadda zasu mayar da hankali kan yaransu.

Ya kara da cewa:

"Muna son tunawa da Hanifa ta hanyar haska Fim din."

An tattaro cewa wasu iyaye sunyi amanna da wannan shiri, kuma wasu sun shirya bada 'yayansu ayi amfani wajen haska Hanifa.

Kara karanta wannan

Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko

Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano
Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel