Matsalar tsaro: Arewa zata ga canji cikin yan watanni masu zuwa, Shugaba Buhari

Matsalar tsaro: Arewa zata ga canji cikin yan watanni masu zuwa, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa yana sane da alƙawurran da ya ɗauka a shekarar 2015
  • Shugaban yace cikin yan watanni kaɗan masu zuwa, mutane za su ga gagarumin canji a arewa maso gabashin Najeriya
  • Buhari ya rantsar da kwamitin gyara da maida yan gudun hijira gidajen su a yankin arewa maso gabas yau a wurin taron FEC

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zasu ga canji a watanni kaɗan masu zuwa musamman a arewa maso gabas.

Buhari ya tabbatar da cewa mutane zasu ga canji daga matsalar ayyukan ta'addanci zuwa zaman lafiya da samun cigaba a yankunan da suke rayuwa.

Shugaban Buhari ya yi wannan furucin ne bisa alƙawarin da ya yi a 2015, na dawo da zaman lafiya a Arewa ta gabas da kuma ɗora yankin kan hanyar cigaba da bunƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Jihohi za su sake sa kafar wando daya da ‘Yan Majalisa kan rigimar dokar zabe

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Matsalar tsaro: Arewa zata ga canji cikin yan watanni masu zuwa, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yace gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da ta cika wannan alƙawarin da ta ɗauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa Femi Adesina ya sanya wa hannu, Buhari yace:

"A farkon zuwan wannan gwamnatin a 2015, na ɗauki alkawarin dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas kuma na ɗora yankin a hanyar cigaba da haɓaka. Ina nan akan bakata."
"Ina tabbatar wa al'ummar arewa ta gabas, musamman yara da gobensu, ba za mu taɓa mantawa da ku ba da kwarin guiwarku a akan mu."
"Ina tabbatar muku a yan watanni masu zuwa zaku ga canji daga rashin tsaro zuwa zaman lafiya, daidaituwar al'amura da cigaba."

Shugaban ya yi wannan jawabi ne yayin rantsar da kwamitin maida yan gudun hijira gidajensu, wanda ya gudana yayin taron majalisar zartarwa na yau Laraba a Aso Villa.

Kara karanta wannan

2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takara ya bugi kirji

Shugaban ya kafa wannan kwamitin ne domin ya yi aikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin dake fama da matsalolin ta'addanci ta hanyar haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki da sauran dabaru.

Shugaba Buhari, wanda ya shata layin cewa babu dalilin gazawa, ya ƙara da cewa tawagar kwamitin za ta yi amfani da dabaru kala daban-daban wajen shawo kan matsalolin baki ɗaya.

Su waye a kwamitin?

Mambobin kwamitin a yankin Arewa ta gabas sun haɗa da ministan Kuɗi, Hajiya Zainab Ahmad, Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, da ministan ayyukan jin ƙai da walwala.

Sauran sune; Mai bada shawara kan tsaro, Sufeta Janar na yan sandan ƙasa, babban hafsan tsaron ƙasa, Daraktan hukumar tsaron farin kaya, Daraktan hukumar Intelligence, da sauran su.

A wani labarin na daban kuma Matasa sun bayyana sunan gwamnan da suke zargi da hannu a harin yan bindiga

Matasan yankin karamar hukumar Shiroro sun zargi gwamnatin jihar Neja da laifi kan harin da yan bindiga suka kai yankin su.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari

A martanin da kungiyar matasa ta yi wa gwamnan jihar, matasan sun ce gwamnati na zargin mutane ne saboda kokarin boye gazawarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel