Hadarin mota a Kano: Mutum 9 sun mutu, 10 sun jikkata yayin da wata mota ta kubce

Hadarin mota a Kano: Mutum 9 sun mutu, 10 sun jikkata yayin da wata mota ta kubce

  • Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane tara yayin da wasu 10 suka jikkata a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano
  • Lamarin ya afku ne a ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, bayan mota ta kubce a hannun direban daya daga cikin motocin da lamarin ya ritsa da su
  • Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ma ya tabbatar da afkuwar lamarin

Kano - An tabbatar da mutuwar mutane tara a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba a jihar Kano.

Hatsarin wanda ya wakana a karamar hukumar Gaya ta jihar ya kuma jikkata mutane 10.

Mummunan hatsarin ya afku ne a wani bangare na babban titin Kano zuwa Maiduguri wanda ake kan gyara kusa da kauyen Sabaru-Laraba a iyakar da ke tsakanin Jigawa da Kano.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jami’in dan sanda ya bindige matashi kan ya sha ‘pure water’ ba tare da izininsa ba

Hadarin mota a Kano: Mutum 9 sun mutu, 10 sun jikkata yayin da wata mota ta kubce
Hadarin mota a Kano: Mutum 9 sun mutu, 10 sun jikkata yayin da wata mota ta kubce Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kakakin hukumar kula da hatsarurruka na tarayya (FRSC) a Jigawa, Ibrahim Gambo, ya bayyana cewa wata tawagar ceto ta hukumar ta kwaso wadanda lamarin ya ritsa da su zuwa asibiti, Premium Times ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’in ya ce hatsarin ya cika ne da wata bas din Toyota Hummer, mai lamba, DRX, 846, XA da wata motar Toyota Sharon mai lamba Dal, 830, XA.

Mista Gambo ya ce daya daga cikin motocin ya kwacewa direban a yayin da yake kokarin guje wa rami sai kawai suka kara da dayan.

Jami’in ya ce maza 17 da mata biyu ne a cikin motocin biyu.

Ya ce dukka wadanda suka mutu maza ne yayin da matan biyu ke cikin wadanda suka jikkata.

Da yake martani kan hatsarin, hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shafukan sadarwar zamani, Bashir Ahmad, a Facebook ya bayyana lamarin a matsayin mai rikitarwa.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Ahmad, wanda ya fito daga garin Gaya, ya ce wadanda abun ya ritsa da su mutanen garinsa ne, wadanda za su je harkokin kasuwanci.

Ya mika ta’aziyya ga sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim, shugaban karamar hukumar, Ahmad Tashi da iyalan mutanen da abun ya ritsa da su.

Ya rubuta a shafin nasa:

"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!
"Yanzu nake samun labarin mummunan hatsarin motan da ya rutsa da wasu ‘yan kasuwar Gaya a hanyar su ta zuwa wajen kasuwancin su. Hatsarin yayi sanadiyyar rasuwar da dama daga cikin ‘yan kasuwar wadanda dukkan su suna da matukar muhimmanci ga garin Gaya da mutanen ta.
"Ina mika sakon ta’aziyya ga Mai Martaba, Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya, Mai Girma, Shugaban Karamar Hukumar Gaya, Hon. Ahmad A. Tashi, ‘yan uwan wadanda hatsarin ya shafa da sauran mutanen gari.
"Ina rokon Allah ya jikan su, ya kuma ba mu hakurin jure wannan babban rashin, sannan Allah ya kiyaye faruwar irin hakan anan gaba."

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Da ɗuminsa: Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano

A wani labarin, jirgin ƙasa dauke da fasinjoji ya markaɗe tirelar siminti da kuma adaidaita sahu wacce aka fi sani da Keke Napep a Kano.

Mummunan al'amarin ya auku ne a titin Obasanjo da ke ƙwaryar birnin Kano a safiyar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Ganau ba jiyau ba waɗanda ke kasuwanci a kusa da layin dogon, ya ce sun ga tirela ta na tafe kusa da dogon yayin da jirgin ƙasan ya dumfaro wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel