Rahoton TI: Mu fa dama mun san gwamnatin APC barauniya ce, Shugaban marasa rinjaye

Rahoton TI: Mu fa dama mun san gwamnatin APC barauniya ce, Shugaban marasa rinjaye

  • Yan jam'iyyar adawa a majalisar wakilan tarayya sun caccaki Gwamnatin Shugaba Buhari kan sabon rahoton Transparency International, TI
  • Kungiyar ta saki sabon rahotonta na shekarar 2021 dake nuna rashawa ta sake muni a Najeriya fiye da baya
  • A kowace shekara, TI na gudanar da bincike kan irin rashawa da cin hanci dake gudana a kasashe duniya

Yan jamiyyar Peoples Democratic Party PDP a majalisar wakilai sun bayyana cewa sabon rahoton kungiyar Transparency International ya nuna gaskiyar da suke fada kan gwamnatin Buhari cewar barauniya ce.

Najeriya ce kasa ta 154 cikin kasashen duniya 180 a rahoton kasashe masu rashawa na 2021.

Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Ndudi Elumelu, yace yayi mamakin yadda Najeriya ce kasar da aka fi rashawa ta biyu a yammacin Afrika.

Shugaban marasa rinjaye
Rahoton TI: Mu fa dama mun san gwamnatin APC barauniya ce, Shugaban marasa rinjaye Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bikin sauya sheka: Dan majalisan APC ya tsallake, ya koma tsagin adawa ta PDP

A jawabin da ya saki ranar Laraba, Elumelu ya ce Gwamnatin APC na fama da rashin basirar samar da ayyukan da zasu amfani yan Najeriya.

Yace:

"Marasa rinjaye a majalisar wakilai sun kadu kan rahoton Transparency International (TI) na 2021 wanda ke nuna Najeriya a matsayin kasa mafi rashawa ta biyu a yammacin Afrika kuma ta 154 cikin 180 a duniya."
"Rahoton TI na jaddada matsayinmu cewa jam'iyyar APC da gwamnatinta barayin banza ne kuma basu da basira da tunanin ayyukan da zasu amfani jama'armu."
"Hakazalika rahoton ya jaddada maganarmu cewa APC gidan rashawa ce, wacce ke boye 'yayanta barayi kuma suna cigaba da satan kudadenmu; wanda haka ya kawo lalacewar tattalin arziki."

Najeriya ce kasa ta 2 a ɓangaren rashawa da cin hanci a Afirka

Mun kawo muku cewa Najeriya ta sake yin kasa da mataki guda a jerin kasashe masu rashawa wato Corruption Perceptions Index (CPI) na 2021 da kungiyar Transparency International (TI) ta fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya milyan 91 na cikin bakin talauci, kungiyar tattalin arzikin Najeriya

Kasar ta ci maki 24 cikin 100 a kididigan na 2021, kamar yadda TI ta wallafa a shafinta na Twitter a @TranperenciITng.

Hakan na nufin cewa rashawa da cin hanci ya kara yawa a Najeriya a bana kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wannan shine karo na biyu a jere da Najeriya ke yin kasa a jerin na TI, a shekarar 2019 Najeriya ta ci maki 26, ta kuma ci 25 a 2020 sannan ta ci 24 a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel