Da Duminsa: An kuma, Najeriya ce kasa ta 2 a ɓangaren rashawa da cin hanci a Afirka

Da Duminsa: An kuma, Najeriya ce kasa ta 2 a ɓangaren rashawa da cin hanci a Afirka

  • Transparency International da ke yaki da rashawa ta fitar da rahotonta na shekarar 2021 inda alkalluman suka nuna cewa ba a samu wani sauyi ba a Najeriya
  • A kididigan na shekarar 2021, Najeriya ce kasa ta biyu a jerin kasashen da ke kan gaba wurin rashawa ta cin hanci a nahiyar Afirka ta Yamma
  • A lokuta da dama gwamnatin Najeriya ta kan rika sukar irin wannan kididigar tana mai cewa Transparency International ba ta san irin nasarorin da kasar ke samu ba a yaki da rashawa

Najeriya ta sake yin kasa da mataki guda a jerin kasashe masu rashawa wato Corruption Perceptions Index (CPI) na 2021 da kungiyar Transparency International (TI) ta fitar a ranar Talata.

Kasar ta ci maki 24 cikin 100 a kididigan na 2021, kamar yadda TI ta wallafa a shafinta na Twitter a @TranperenciITng.

Kara karanta wannan

Bayan an yi waje da zakarun 2019, Super Eagles sun san da wa za su hadu a AFCON

Hakan na nufin cewa rashawa da cin hanci ya kara yawa a Najeriya a bana kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Da Duminsa: Najeriya ce kasa ta 2 a ɓangaren rashawa da cin hanci a Afirka ta Yamma
Najeriya ta sake dilmiyawa kasa a jerin kasashe da ke kan gana wurin rashawa a duniya. Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan shine karo na biyu a jere da Najeriya ke yin kasa a jerin na TI, a shekarar 2019 Najeriya ta ci maki 26, ta kuma ci 25 a 2020 sannan ta ci 24 a 2021.

Kungiyar na TI tana amfani da CPI don gwada matsayin rashawar a kasashe da dama a duniya. Transparency International na bada maki ne daga 0 zuwa 100. Sifiri (0) na nufin kasar da tafi rashawa, 100 kuma kasa mara rashawa.

A wannan jerin Najeriya ita ce ke mataki na 149 cikin kasashe 180 da aka duba su a Afirka, hakan na nufin ita ce kasa na biyu mafi muni a bangaren rashawa ta cin hanci a Afirka.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Buhari ta taimakawa mutane sama da 500, 000 inji Dr. Isa Pantami

Wannan jerin sunayen na iya nufin cewa rashawa da cin hanci ya kara munana a kasar cikin shekaru.

Martanin Najeriya

A bangare guda, hukumomi a Najeriya sun dade suna nuna rashin amincewarsu da kididigar ta TI da ke nuna rashawa da cin hanci na karuwa a kasar.

Ta yi ikirarin cewa TI din ba ta san irin nasarorin da gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari ta samu a bangaren yaki da rashawa ba.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, ya ce rahoton na TI-CPI bai yi la'akari da manyan nasarorin da kasar ta samu a bangaren yaki da rashawa ba.

Ministan ya kuma saka alamar tambaya a kan inda aka samo alkalluman da TI ta yi amfani da su.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel