Yan Najeriya milyan 91 na cikin bakin talauci, kungiyar tattalin arzikin Najeriya

Yan Najeriya milyan 91 na cikin bakin talauci, kungiyar tattalin arzikin Najeriya

  • Sabbin mutum milyan takwas sun dilmiya cikin talauci a shekarar 2021 da ta kare, cewar NESG
  • Kungiyar tattalin arziki ta ce jimillan yan Najeriya dake fama da talauci yanzu ya haura milyan casa'in
  • An janyo hankalin gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyin inganta rayukan yan Najeriya a 2022 maimakon siyasa

Abuja - Kungiyar tattalin arzikin Najeriya, NESG, ta bayyana cewa yan Najeriya milyan 91 ke cikin bakin talauci yanzu haka a fadin tarayya.

Shugaban kungiyar, Mr. Asue Ighodalo, ya bayyana hakan ranar Talata, a taron kaddamar da takardar hasashen tattalin arzikin 2022, a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, talauci ya zama wani sabon cuta mai zaman kansa wanda ya fi Korona hadari dubi ga adadin mutanen da suka kamu.

Yace:

"Bankin duniya ta yi bayanin cewa tsakanin watar Yuni da Nuwamban 2021, karin mutum milyan daya sun tsunduma cikin talauci, hakan na nafin cewa mutum milyan 8 aka jefa talauci a 2021 kuma adadin matalauta a Najeriya ya kai 91 million."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

"Mutum milyan 91 kenan suka kamu da cutar Talauci, wacce ta fi illa fiye da COVID-19."

Bakin talauci,a Najeriya
Yan Najeriya milyan 91 na cikin bakin talauci, kungiyar tattalin arzikin Najeriya
Asali: UGC

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen inganta rayukan jama'arta a shekarar 2022 maimakon mayar da hankali kan lamuran siyasa.

A cewar shugaban kungiyar, idan gwamnati ta bari siyasa ya dauke mata hankali, za'a yi asarar yan nasarorin da aka samu.

Mr. Asue Ighodalo, ya yi kira ga yan Najeriya su zabi mutumin kirki wanda aka tabbatar zai iya inganta tattalin arzikin kasar.

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

Tsohon Shugaban kasan mulkin Soja, Janar AbdulSalami Abubakar, ya yi gargadi game da shirin kara farashin litan man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

A jawabin da ya gabatar ranar Alhamis a taron tattaunawa kan halin da kasa ke ciki da Daily Trust ta shirya a Abuja, tsohon Sojan yace hakan na da hadari.

A cewarsa, sama da yan Najeriya milyan 18 yanzu haka na fama da bakar talauci da bai kamata ba kuma annobar COVID-19 ta sake tsananta lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel