Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, kwatankwacin ƙarfin tattalin arzikin Senegal

Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, kwatankwacin ƙarfin tattalin arzikin Senegal

  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya samu karin kimanin Dala Biliyan 1.3 cikin makonni ukun farkon 2022
  • Hakan ya kawo jimillar arzikin attajirin zuwa kimanin Dalar Amurka Biliyan 20.4, kadan ya rage ya kai karfin tattalin arzikin Senegal da ke Dala Biliyan 24.9
  • Dangote ya samu karin arzikin ne bayan sayar da hannu jari na kamfanin siminti na Dangote kuma ana sa ran arzikinsa zai bunkasa bayan kammala matatan man fetur dinsa

Alhaji Aliko Dangote ya samu karuwar arziki da kimanin Dala biliyan 1.3 (N539,435,000,000.00) a farkon shekara zuwa ranar 21 ga watan Janairu, a cikin wannan lokacin masu hannu jari a kamfanin simintin Dangote sun samu alheri, rahoton Premium Times.

A halin yanzu arzikin sa ya tasanma na Dala biliyan 20.4 a cewar kididigar Biloniyoyi na Bloomberg a ranar Juma'a, hakan na nufin arzikin na dan kasuwan mafi arziki a Afirka ya kai kusan karfin tatttalin arzikin kasar Senegal da Bankin Duniya ta kiyasta ka Dalla biliyan 24.9.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, kwatankwancin ƙarfin tattalin arzikin Senegal
Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, ya kusa kai ƙarfin tattalin arzikin Senegal. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Dangote ya samu wannan karuwar arzikin ne bayan masu saka jari sun siya hannun jari a kamfaninsa karo na biyu a wannan makon, inda suke fatan hannun jarin kamfanin zai kara daraja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga farkon shekara zuwa yanzu, kamfanin simintin Dangote ya samu karin daraja da kashi 11 cikin 100, ya zama kamfanin Najeriya mafi samun riba a kasuwan hada-hada da darajar N4.9 tiriliyan a ranar Juma'a.

Kamfanin simintin shine kusan rabin arzikin Dangote, a yanzu kowanne hannun jari guda ya kai N265.7.

Bloomberg ta ruwaito cewa attajirin dan kasuwan yana cikin biloniyoyi 35 mafi arziki a duniya da arzikinsu ya karu a watan Janairu. Wanda ya fi samun karin arziki a cikin kankanin lokaci shine Gautam Adani na India da arzikinsu ya karu da $13 biliyan yanzu yana da $89.5 biliyan.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma

Ana fatan arzikin Dangote zai samu karuwa sosai a cikin shekarar 2022 bayan ya kammala gina matatan man fetur dinsa da ya lashe kimanin $19 biliyan.

Matatan zai zama matata daya-tilo mafi girma a duniya inda zai rika tace ganga 650,000 a kowanne rana idan ya kammala.

Attajirin ya bayyana wa Financial Times cewa yana da niyyar siyan kungiyar kwallon kafa a Ingila idan ya kammala gina matatan man fetur din.

Sunaye Da Hotuna: Bakaken Fata 5 Da Suka Fi Kudi a Duniya

A cikin sunayen biloniyoyin duniya na jaridar Forbes, akwai biloniyoyi 2,775 a duniya kuma fiye da 10 daga cikinsu bakaken fata ne.

Rahoton nan ya jero mutane 5 na masu kudin duniya wadanda duk bakaken fata ne, har ila yau har da sana’o’in da suke yi da suka kawo musu dukiyoyin da suka mallaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel