Ameachi: Sarkin Daura Zai Naɗa Ministan Buhari ‘Dan Amanar Daura’

Ameachi: Sarkin Daura Zai Naɗa Ministan Buhari ‘Dan Amanar Daura’

  • Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, zai nada Ministan Sufuri na Najeriya, Mr Rotimi Amaechi, sarautar Dan Amnar Daura
  • Ana sa ran za a yi bikin nadin sarautar ne a ranar Asabar 5 ga watan Fabrairun shekarar 2022 idan ba samu sauyi ba
  • Bisa ga alamu, masarautar ta Daura ta karrama Ameachi da sarautar ne saboda ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi a Daura

Jihar Katsina - Masarautar Daura a Jihar Katsina ta amince za ta karrama Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da sarauta ta gargajiya, Daily Trust ta ruwaito.

Idan har ba a samu wani sauyi ba daga baya, Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, zai nada Ministan sarautar Dan Amanar Daura, a ranar Asabar 5 ga watan Fabarairun 2022.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan siyasa 4 da suka ziyarci tsohon shugaban kasa IBB domin kama kafar 2023

Ameachi: Sarkin Daura zai nada ministan Buhari ‘Dan Amanar Daura’
Ameachi: Sarkin Daura zai nada ministan Buhari ‘Dan Amanar Daura’. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Tuni dai an fara tura wa bakin da ake sa ran za su hallarci taron katin gayyata yayin da masarautar ke cigaba da shirye-shiryen bikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokuta da dama, Sarkin Daura ya sha nanatawa cewa masarautar ba ta taba samun ayyukan ci gaba irin lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba, wanda dan asalin garin ne.

Daya daga cikin manyan ayyukan shine Jami'ar Sufuri, wacce ministan ya taka muhimmin rawa don ganin an gina ta a Daura.

Ana iya fassara Sarautar Dan Amana a matsayin wanda aka amince da shi a waje, ta yi wu Sarkin ya yi amfani da kusancin Amaechi ne da Shugaba Buhari.

An fara nada Amaechi matsayin minista ne a shekarar 2015 sannan aka sake nada shi a 2019, kuma ana masa kallon daya daga cikin makusantan Shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

Ameachi ya rike mukamin shugaban yakin neman zaben Buhari a 2015, kuma ya cigaba da rike mukamin yayin da Buhari sai sake tara a 2019 bayan shekaru hudu na wa'adin farko.

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

A wani rahoton, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel