Kano: 'Yan sanda sun gayyaci Muaz Magaji, korarren kwamishinan Ganduje, kwararren mai sukar gwamnan

Kano: 'Yan sanda sun gayyaci Muaz Magaji, korarren kwamishinan Ganduje, kwararren mai sukar gwamnan

  • Fitaccen mai sukar mulkin Gwamna Ganduje na jihar Kano, kuma korarren kwamishinan ayyukan na jihar, ya samu goron gayyata daga 'yan sandan jihar
  • Muazu Magaji, tsohon na hannun daman gwamnan, ya ce 'yan sanda sun gayyace sa ne kan korafi da gwamnatin jihar ta kai musu a kan sa
  • Sai dai Magaji ya ce ba ya Kano, amma babu shakka zai amsa gayyatar a ranar Talata idan ya koma jihar, don babu abinda zai guje wa

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci Muazu Magaji, tsohon kwamishinan ayyuka a mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.

A yayin tattaunawa da Daily Trust, Magaji ya ce sashin SBI na siyasa na rundunar 'yan sandan ne suka gayyace sa, amma bai sanar da dalilin gayyatar ba.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Kano: 'Yan sanda sun gayyaci Muaz Magaji, korarren kwamishinan Ganduje kuma kwararren mai sukar gwamnan
Kano: 'Yan sanda sun gayyaci Muaz Magaji, korarren kwamishinan Ganduje kuma kwararren mai sukar gwamnan. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Na samu kira kan cewa suna son in bayyana a gaban su. Na tambaye su a kan mene ne kuma sun sanar da ni cewa zan san abinda ke faruwa idan na je.
"A lokacin da na matsa, sun ce gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da korafi a kai na," yace.

A yayin da aka tambaya ko ya amsa gayyatar, tsohon kwamishina ya ce a halin yanzu ya na Abuja kuma zai amsa gayyatar idan ya koma jihar Kano a ranar Talata.

"Me na ke guje wa? babu shakka zan amsa gayyatar gobe," ya tabbatar.

Sai dai kuma, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa bai samu damar yin tsokaci kan lamarin ba.

Magaji ya kasance wanda bakin sa ba ya shiru kan al'amuran yau da kullum da ke faruwa a jihar Kano tun bayan da aka tube sa a matsayin kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasar Mali wanda aka yi wa juyin mulki, Ibrahim Keita, ya rasu

Gwamnan ya nada tsohon kwamishinan a matsayin hadiminsa kan al'amuran bututun iskar gas na AKK bayan tube sa a matsayin kwamishina, amma aka fatattake sa daga baya.

Daga lokacin, korararren kwamishinan ya dinga caccakar Ganduje da mulkinsa a kafar sada zumunta ta Facebook.

A halin yanzu, Magaji mamba ne na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) tsagin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau.

Ganduje ya ziyarci shugaban APC na tsagin Shekarau, Ahmadu Danzago

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Lahadi, ya kai ziyarar ta'aziyya ga shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Ahmadu Danzago, wanda ya karba kujerar a kotu.

Ya kai wa Danzago ziyarar ne sakamakon mutuwar da da yayansa ya yi a ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.

An zabi Danzago a matsayin shugaban APC a jihar a zaben da aka yi na ranar 18 ga watan Oktoba, 2021 wanda tsagin tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau suka yi.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel