Muhimman batutuwa 10 da Buhari ya yi magana a kansu yayin hirar da aka yi da shi

Muhimman batutuwa 10 da Buhari ya yi magana a kansu yayin hirar da aka yi da shi

  • A ranar Laraba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu tattaunawa da gidan talabijin din Channels wanda ya yi maganganu da dama
  • Yayin tattaunawar Shugaban ya yi tsokaci akan abubuwa da dama da su ka shafi gwamnatinsa da tattalin arzikin kasa har da tsaro
  • A cikin wannan labarin za mu zayyano matsalolin da aka tattauna da shi a kan su da kuma tsokacin da ya yi dangane da matsalolin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba 5 ga watan Janairun 2022.

Yayin hirar, shugaban kasa ya yi maganganu da tsokaci iri-iri a kan gwamnatinsa, tattalin arzikin kasa da tsaron ‘yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Batun sakin Kanu, Ƴan Sandan Jiha da wasu abubuwa 8 da Buhari ya yi magana kansu yayin hira da aka yi da shi
Muhimman batutuwa 10 da Buhari ya yi magana a kansu yayin hirar da aka yi da shi. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Batun kasafin kudin 2023: Buhari ya ce ba za a samu matsala ba saboda APC

Mun lissafo abubuwa 10 wadanda Buhari ya yi magana a kan su yayin tattaunawar a cikin gidan gwamnati.

1. Ba mafita bane samar da ‘yan sandan jiha

Shugaban kasa Buhari ya ce samar da ‘yan sandan jiha ba zai taba zama mafita ba ga kasar nan.

A cewarsa ya kamata kasa ta fara gyara alakar da ke tsakanin shugabancin

kananun hukumomi da gwamnoni.

Ya yarda da cewa akwai wata iyaka tsakanin gwamnoni da kuma shugabannin kananun hukumomi kuma daga hakan ne a ke samun cikas wurin kakkabo rashin tsaro.

Buhari ya kara da cewa kada a raina matsayin shugabannin gargajiya, saboda sun san ‘yan uwan ‘yan ta’addan da ke karkashin ikon su.

2. Kanu: Ba za a sake shi ba

Dangane da batun shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, shugaban kasa ya ce ba za a rangwanta masa ba.

Ya kara da cewa ba zai sanya kansa a harkar shari’a ba don duk wani dan Najeriya ya san ba ya shiga irin wadannan harkokin.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

A cewar Buhari:

“Za a saurare shi a kotu. Ga wadanda su ke son a sake shi, ba za mu iya sakin shi ba.
“Akwai yuwuwar samun mafita idan kowa ya natsu ya yi abinda ya dace. Ba zai yuwu ka fita ka dinga surutai marasa kyau dangane da tattalin arzikin kasa ko tsaro ba kuma ka na tunanin ba za a titsiye ka ba.”

3. Yadda za a bullo wa ‘yan ta’adda

Yayin magana dangane da ‘yan bindiga, shugaban kasa ya lashi takobin yaki da ta’addancin da kasar nan ke fama da shi musamman yankin arewa maso yamma.

“Mun yi maganganu da shugabannin tsaro da sifeta janar na ‘yan sanda kuma za a bi bayan duk wasu ‘yan ta’adda a ragargaje su,” in ji Buhari.

4. Zan sa hannu a kan dokar gyara akan zabe idan...

Dangane da nuna damuwarsa akan gyare-gyare akan dokokin zabe, shugaba Buhari ya ce a shirye yake da ya sa hannu matsawar majalisar tarayya ta yi duk abinda ya ce.

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

Ya kara da cewa matsawar aka samu hadin kai wurin ‘yan takara, za a iya yin zaben fitar da gwani a kaikaice maimakon dayan wanda ake yi a baya ga jam’iyyun siyasa.

A cewarsa, wajibi ne a ba ‘yan Najeriya damar yin demokradiyyarsu ta gaskiya.

5. Mu na maraba da duk wanda zai taimaka wa Najeriya da kayan more rayuwa

Yayin da ya yi tsokaci akan bashin China, shugaban kasa ya kare matakin gwamnatinsa inda ya ce ana maraba da duk wanda zai tallafa wa Najeriya, ya ce:

“Mu na amsar bashi a inda ya dace. Na fada maka abinda a baya ya ke aukuwa idan mutum zai yi tafiya tsakanin Legas zuwa Ibadan balle sauran yankunan kasa.
“Amma mun samu mutanen kasar China da za su yi mana titinan jirgin kasa da hanyoyi, sai mu ce bama so? Idan muka kyale watarana a kafa za a dinga zuwa daga Legas zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani

“Don haka muna maraba da ‘yan China, da duk masu shirin taimakon mu baya ga su muna maraba.”

6. Ina jin PDP na ke ayyana rashin nasara a zuciyata

Bayan an tambaye shi a kan jam’iyyar PDP, ya ce rashin nasara ke fara zuwa masa idan ya ji an kira sunan jam’iyyar.

Sai dai hakan ba abin mamaki bane sakamakon yadda ya dade yana daura duk wata matsalar kasar nan ga jam’iyyar.

7. Ina sane da wahalar da ‘yan Najeriya suke sha

Dangane da mummunan yanayin da ‘yan Najeriya suke ciki, shugaban kasa ya ce ya san azaba da radadin da ‘yan Najeriya su ke fuskanta karkashin mulkinsa.

8. Wajibi ne ‘yan Najeriya su koma gona

Yayin kawo mafita a kan wahalar da ake sha, shugaban kasa ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su koma gonakin su.

“Mun gano cewa ba a yi latti ba, ya kamata mu koma noma da kiwo don hakan ne zai kawo mafita da nasarori gare mu,” a cewar shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

9. Ba kammala karatu ne ke ba mutum damar aikin gwamnati ba

Kamar yadda shugaba Buhari yace, wajibi ne matasa su mike tsaye su dogara da kawunansu kuma su daina kallon ilimi a matsayin matakin samun aikin gwamnati.

“Ina ma yadda su ke zuwa makarantu, su na aiki tukuru; bayan samun digirin ba sa tunanin batun samun ayyukan gwamnati,” a cewarsa.

10. Ba zan fadi sunan wanda na fi son ya gaje ni ba

Ba kamar yadda sauran shugabannin siyasa su ke yi ba yayin kammala shekarunsu na karshe, shugaba Buhari ya ki bayyana sunan wanda ya fi so ya gaje shi.

Yayin bayar da amsa a kan tambayar wanda ya ke so ya gaje shi, Buhari murmushi ya yi ya ce: “a’a, ba zan fadi sunan wanda nake so ya gaje ni ba saboda za a iya cire shi idan na fadi. Gara in yi shiru.”

Shugaban kasar ya ce manufarsa shi ne ya tabbatar gwamnatinsa ta tsayar da gaskiya don hana sace-sace da kuma duk wasu ayyukan da ba su dace ba hakan ya fi muhimmanci ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan ya kammala wa'adin mulkinsa lafiya domin 'tsufa ya fara kama shi', Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda ya cika shekaru 79 a ranar 17 ga watan Disamban 2021, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambaya a tattaunawa da aka yi da shi a NTA, a ranar Alhamis.

"Game da shekaru na, ina ganin sa'o'i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel