Bashir: Wanene hamshakin mamallakin kamfanin Mafab da ya samu lasisin amfani da 5G?

Bashir: Wanene hamshakin mamallakin kamfanin Mafab da ya samu lasisin amfani da 5G?

  • Kafin yau, 'yan Najeriya masu tarin yawa basu taba jin sunan Mafab Communications ba, kamfanin sadarwa da aka kirkiro a ranar 8 ga Yulin 2020
  • Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya ta bai wa kamfanin lasisin ayyukan sadarwa a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba
  • Kamfanin sadarwa na Mafab da MTN ne kadai kamfanoni biyu na Najeriya da suka samu nasarar samun lasisin 5G a kasar nan

Idan ka kira kamfanin sadarwa na Mafab ga abokan ka ko kuma ka yi kokarin kiran sunan Dr. Musbahu Mohammad Bashir, babu shakka za a ce maka "waye shi?"

Amma kuma, bayan hukumar kula da sadarwa ta Najeriya ta sanar da Kamfanin sadarwa na Mafab a matsayin daya daga cikin kamfanonin da suka yi nasarar samun lasisin 5G a kasar nan a ranar Litinin 13 ga watan Disamba a Abuja, Bashir ya na daya daga cikin wadanda ake ta neman karin bayani a kan shi a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Bayan karbar N8m na fansa, 'yan bindiga sun sheke ma'aikacin lafiya da manajan masana'anta

Lasisin 5G
Bashir: Wanene hamshakin mamallakin kamfanin Mafab da ya samu lasisin amfani da 5G? Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kamfanonin biyu za su biya jimillar kudi har $273.6 miliyan wanda yayi daidai da (N134 biliyan) zuwa ranar 22 ga watan Fabrairun 2022.

Wannan na zuwa ne bayan watanni 16 da Kamfanin sadarwa na Mafab ya yi rijista da kamfanonin Althani Group, wani kamfani mai zaman kansa.

Bayanai daga Corporate Affairs Commission ya nuna cewa kamfanin sadarwa na Mafab zai samar da hanyar sadarwa ta murya, bidiyo da data a duniya.

Bashir shi ne shugaban Althani Group of Companies. Shugaban ya na cikin mambobin majalisar zartarwa ta bankin Jaiz kuma daraktan kamfanonin Be to Drill Nigeria Limited tun 1995, Offshore Technologies International Limited tun 1995 da kuma Resource Capital Group tun 1995.

Hakazalika, shi ne shugaban Cobalt International Services.

Ta yaya Mafab sabon kamfanin sadarwa suka bige Glo, Airtel da sauransu?

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

Tun farko Legit.ng ta ruwaito yadda kamfanin sadarwa na Mafab Communications Limited ya yi nasarar samun lasisin 5G inda ya bige fitattun kamfanonin sadarwa na Glo, Airtel da sauransu.

Mafab ya fuskanci kalubale daga manyan kamfani sadarwa na Airtel da MTN. Abun mamakin shi ne yadda Glo da 9mobile suka yi warwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel