'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa sun sanar da yadda 'yan banga suka bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa
  • Miyagun sun kutsa wani gida a yankin Balms da ke Song inda suka kashe maigidan tare da sace diyarsa mai suna Queen Bakomi
  • A yayin kai musu kudin fansa ne 'yan banga suka yi kwanto sannan suka bude musu wuta tare da kashe daya da kuma ceton Queen

Song, Adamawa - 'Yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da 'yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga 'yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jihar.

Kara karanta wannan

Jigawa: Ɗalibai 10 Sun Kutsa Gidan Wani Mutum Cikin Dare Sun Ɗaure Shi Sun Masa Askin Dole

Rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoto daga 'yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa 'yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa," Nguroje ya ce.
'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa
'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya ce rundunar ta na bincike kan lamarin amma majiya mai karfi kuma dan banga a kauyen Murke, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, a ranar 20 ga watan Augusta ne miyagu suka kutsa yankin Balms.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Majiyar ta ce yayin harin, miyagun sun kutsa gidan wani Bakomi Andrawus inda suka bindige shi kuma ya mutu a take.

Bayan kashe Bakomi Andarawus, masu garkuwa da mutanen sun sace diyarsa, Queen Bakomi.
Ta kwashe kwanaki shida a wurinsu kuma sun bukaci karbar naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa kafin su sake ta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Yayin da iyalan mamacin suke kokarin birne shi, sun tattara kudi har N170,000 domin karbo ta," majiyar tace inda ta kara da cewa sun roki masu garkuwa da mutanen kuma sun amince da su kai kudin haka.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun umarci wakilan wacce suka sace da ya kai kudi wani daji inda za su karba.

Ganin tashin hankalin da iyalan ke ciki, 'yan banga sun yanke hukuncin tunkarar masu garkuwa da mutanen. Sun yi kwanto a dajin wurin karfe 8:30 na dare kafin masu karbar kudin su iso," yace.

Ya ce 'yan bangan sun budewa miyagun wuta inda suka kashe daya yayin da suka kubutar da wacce aka sace cike da nasara.

Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata

A wani labari na daban, Peter Aboki, tsohon mataimakin shugaban makarantar noma, kimiyya da fasaha da ke Lafia, jihar Nasarawa, ya maka tsohon kwamishinan noma, Alanana Otaki a babbar kotun Lafia bisa kwace masa matarsa da yayi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon harin Jihar Benue ya yi ajalin rayukan mutane 8

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, matar da ake rikici a kan ta, Felicia Aboki, ta kai karar mijin ta kotu ta na bukatar a warware aurensu mai shekaru 18.

A ranar Litinin, lauyan Mr Aboki, Shikama Shyeltu, ya bukaci a dakatar da karar da matar Aboki ta kawo don yanzu haka ana batun ta na da wata alaka duk da ta na da aure da tsohon kwamishinan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel