Barayin da suka sace Liman da wasu 10 lokacin sallar Asuba a Neja Sun nemi a lale musu Miliyoyi

Barayin da suka sace Liman da wasu 10 lokacin sallar Asuba a Neja Sun nemi a lale musu Miliyoyi

  • Yan bindigan da suka sace masallata yayin sallan Asuba a jihar Neja, sun nemi a biya miliyan N60m kuɗin fansa
  • Maharan sun kashe aƙalla mutum 18 yayin harin, sannan suka sace limamin masallacin da kuma wasu mutum 10
  • Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigan sun harbe wata mata har lahira lokacin harin, saboda tsoratar da ta yi

Niger - Maharan da suka yi garkuwa da masallata a ƙauyen Maza-Kuka, ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja, sun nemi a tattara musu miliyan N60m kuɗin fansa.

Dailytrust ta rahoto cewa yan bindiga sun kai harin ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin lokacin da mutane suke tsaka da sallar Asuba.

Jihar Neja
Barayin da suka sace Liman da wasu 10 lokacin sallar Asuba a Neja Sun nemi a lale musu Miliyoyi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Maharan sun kashe aƙalla mutum 18 a lokacin, yayin da suka yi awon gaba da wasu da dama.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

Mutum nawa aka yi garkuwa da su?

Wani majiya daga ƙauyen, wanda ya yi magana cikin kwarin guiwa, ya shaida wa manema labarai cewa mutum 11 suka sace, cikinsu har da limamin masallacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BBC Hausa ta rahoto mutumin Yace:

"Sun kira waya jiya, kuma sun bukaci a tattara musu miliyan N60m kuɗin fansa. A halin yanzun bamu san ya zamu yi ba."
"Duk da cewa masallacin da lamarin ya shafa na Jumu'a ne, amma limamin dake jagorantar salloli biyar na kowane yini yana cikin waɗan da aka sace tare da wasu 10."

Shin dagaske an kashe mace a harin

Rahoto ya tabbatar da cewa cikin waɗanda maharan suka hallaka akwai wata matar aure guda ɗaya.

Wani majiya mai ƙarfi, wanda ya tabbatar da cewa matar abokinsa ce, yace:

"Lokacin da suka kawo harin ta tsorata kuma ta yi ƙara tare da kokarin tserewa. A wannan lokacin ne suka harbe ta, ta mutu nan take."

Kara karanta wannan

Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

"Amma bayan wannan, yan bindiga ba su taba mace ba, duk waɗanda lamarin ya shafa baki ɗaya maza ne."

A wani labarin kuma Bayan kai wannan harin ne Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

Rahoto ya nuna cewa yan bangan sun hallaka wani hakimi da ɗan uwansa bisa zarginsu da hannu a harin masallaci.

Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya roki gwamnatin tarayya ta faɗaɗa luguden wutan sojoji kan yan bindiga zuwa jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel