Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

  • Wasu yan banga sun ɗauki fansa kan harin da aka kai masallaci a jihar Neja, inda aka kashe mutane tare da sace wasu
  • Rahoto ya nuna cewa yan bangan sun hallaka wani hakimi da ɗan uwansa bisa zarginsu da hannu a harin masallaci
  • Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya roki gwamnatin tarayya ta faɗaɗa luguden wutan sojoji kan yan bindiga zuwa jihar Neja

Niger - Wasu yan banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja awanni kaɗan bayan yan bindiga sun hallaka mutane dake sallar Asuba a garin Maza-Kuka.

Aminiya ta rahoto cewa Hakimin yankin Adogon, Alhaji Sa'idu Abubakar da ɗan uwansa, Alhaji Salihu Abubakar, sun rasa ransu ne a harin da ake tunanin na ɗaukar fansa ne.

Tun a baya dai, wasu mahara sun buɗe wa mutane dake sallar Asuuba wuta, inda suka ƙashe aƙalla mutum 18 tare da sace wasu a garin Maza-Kuka, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Barayin da suka sace Liman da wasu 10 lokacin sallar Asuba a Neja Sun nemi a lale musu Miliyoyi

Jihar Neja
Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Meyasa yan Banga suka kashe hakimin?

Bayan wannan harin ne, yan banga suka kai hari garin Adogon Malam, inda suka kashe mutanen biyu saboda zargin suna da hannu a harin Masallaci.

Garuruwan biyu na Maza-Kuka da Adogon Malam suna kusa da juna kuma duk suna ƙarƙashin ƙaramar hukumar Mashegu a jihar.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan ƙasar nan, reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin guda biyu.

Sai dai a jawabinsa kakakin yan sandan yace a halin yanzun hukumar yan sanda ba ta da tabbacin kon hari na biyu yana da alaƙa da na farko.

A kawo mana ɗaukin sojoji - Gwamna

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya bukaci FG ta taimaka da ƙarin jami'an sojoji domin magance hare-haren yan bindiga a jiharsa, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan siyasan Najeriya ne suke rura wutar rikici a Jos, Shugaban gwamnonin Arewa

Gwamnan ya yi wannan kira ne bayan harin da aka kai masallaci, inda ya bukaci FG ta faɗaɗa aikin luguden wutan sojoji a kan yan bindiga zuwa Neja.

Abubakar Bello yace:

"Mun fara tattaunawa da hukumomin tsaro, domin lalubo hanyoyi da dabarun kawo karshen hare-haren yan bindiga."

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina

Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki ƙauyen Unguwar Samanja a Faskari ana gab da sallar Magrib

Wani mazaunin Daudawa ya koka kan yadda yan bindiga ke cigaba da aikin ta'addancinsu a Faskari duk da matakan da gwamnati ta ɗauka Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel