An daure makiyayi daurin rai da rai bisa laifin gwada kashe wani da mallakar mugun makami

An daure makiyayi daurin rai da rai bisa laifin gwada kashe wani da mallakar mugun makami

  • Babbar kotun jihar Ekiti da ke zama a Ado Ekiti, ta yanke wa Muhammadu Abubakar, makiyayi mai shekaru 32 daurin rai-da-rai
  • Alkalin kotun ya zartar da hukuncin ne bayan samun Abubakar da laifin yunkurin aikata kisan kai da mallakar mugun makami
  • An tattaro cewa ya shiga gonakin mutanen da ya yi kokarin kashewa tare da dabobbinsa

Jihar Ekiti - Babbar kotun jihar Ekiti da ke zama a Ado Ekiti, ta yanke wa wani makiyayi mai shekaru 32, Muhammadu Abubakar, daurin rai-da-rai.

An yanke wa Abubakar hukuncin ne bayan samunsa da laifin yunkurin aikata kisan kai da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba, jaridar Thisday ta rahoto.

An daure makiyayi daurin rai da rai bisa laifin gwada kashe wani da mallakar mugun makami
An daure makiyayi daurin rai da rai bisa laifin gwada kashe wani da mallakar mugun makami Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Da yake zartar da hukunci, Justis Adekunle Adeleye ya ce:

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

“An kama wanda ake karar da aikata laifin da ake tuhumarsa a kai, don haka an yanke masa daurin rai-da-rai.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bisa ga tuhumar da ake masa, a watan Afrilun 2019, Abubakar ya yi yunkurin kashe wani Cif Samuel Amaa da wasu a Aba Cotonou, Omu Ekiti, a karamar hukumar Oye na jihar Ekiti.

An tattaro cewa ya aikata hakan ne yayin da yake kiwon dabbobinsa a gonakinsu.

Da yake koro jawabi a gaban kotun, daya daga cikin wadanda abun ya shafa ya ce, an kalubalanci wanda ake karan yayin da yake kiwon dabbobinsa a gonarsu ta rogo sai ya fusata da yadda ake masa tambayoyin.

An ce nan take sai Abubakar ya ciro bindigarsa sannan ya kama harbinsu.

Sai dai kuma an ce mazauna yankin sun sha karfin Abubakar inda suka kama shi sannan suka mika shi ga 'yan sanda domin bincike, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Domin tabbatar da shari'arsa, mai gabatar da kara, Taiwo Ajibulu, ya kira shaidu hudu sannan ya gabatar da wata bindiga, harsashi mai rai da bayanai da sauransu don hukunta shi.

Yayin da wanda ake kara ya yi magana don kare kansa ta hannun lauyansa sannan bai kira kowani shaida ba.

Laifukan sun sabawa sashe na 320 na dokar laifuka, Cap. C16 Dokokin Jihar Ekiti, 2012 da 3 (1) na Dokar fashi da makami, Cap.R11, Vol.14, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

A gefe guda, Yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani makiyayi mai shekaru 25, wanda aka zargi ya kutsa cikin gonakin wasu ya lalata kayan gona na N200,000 a kauyen Takatsaba da ke karamar hukumar Suletankarkar a jihar.

Jaridar The Guardian ta ruwaito ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin ciin sanarwar da ya fitar a Dutse, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya

Shiisu ya kuma kara da cewa yan sanda sun kama shanu 73 da awaki 13 da suka kutsa gidan wasu gonaki a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel