Shugabancin kasa a 2023: Tinubu na kara samun goyon baya, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani ya ziyarci babban jigon APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu a gidansa na Lagas
- A yayin ziyarar, Sanatan ya jinjinawa Tinubu kan gudunmawarsa ga ci gaban dimokradiya da shugabanci nagari a kasar
- Yayin da yake yi masa fatan alkhairi, dan siyasan na Najeriya ya bai wa jigon na APC kwafin sabon littafinsa
Ikoyi, Lagos - Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu, na ci gaba da tarban baki tun bayan dawowarsa daga kasar Ingila.
Bako na baya-bayan nan da ya tarba shine tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, wanda ya ziyarce shi a gidansa na Ikoyi, Lagos, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, don yi masa fatan alkhairi bayan dawowarsa daga Ingila.
Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP
Sanatan ya yaba da gudunmawar da Bola Tinubu ke bayarwa wajen ci gaban damokradiya da shugabanci nagari a Najeriya, rahoton jaridar The Guardian da PM News.
Ya ce wadannan gudummawa sune manyan ginshiki da zasu taimaka masa wajen ci gaba.
Nnamani ya kuma gabatarwa Tinubu da sabon littafinsa mai suna “Standing Strong: Legislative Reforms, Third Term and Other Issues of the Fifth Senate,” wanda ake shirin gabatarwa a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, a Abuja.
Rikakken ‘Dan adawa Fayose ya kai wa Bola Tinubu ziyara har gida, ya fadi abin da ya kai shi
A baya mun kawo cewa, a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, 2021, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya kai wa jigon jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ziyara.
Ayo Fayose ya je har gidan babban jigon na jam’iyyar APC da ke Bourdillon, garin Ikoyi, jihar Legas.
Tsohon gwamnan na Ekiti, kuma daya daga cikin manyan jagororin PDP ya ajiye batun siyasa a gefe guda, ya je ya duba lafiyar Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng