Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata

  • 'Yan bindiga sun sako dalibai 3 daga cikin wadanda suka sata a makarantar horar da fastoci da ke Jema'a, Kaduna
  • Shugaban makarantar, Rabaren Fada Emmanuel Uchecukwu Okolo, ya tabbatar da hakan a daren Laraba
  • Ya bayyana godiyarsa ga Ubangiji da wadanda suka taya su da addu'a tare da fatan samun 'yancin sauran

Jema'a, Kaduna - Uku daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da aka sace na Christ the King Major Seminary a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna sun samu 'yancinsu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruiwaito, shugaban makarantar, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin su da aka yi a daren Laraba.

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata
Kaduna: 'Yan bindiga sun sako 3 daga cikin daliban makarantar horar da limaman coci da suka sata. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Ya ce cocin za ta cigaba da addu'a tare da fatan a sako sauran daliban da ke hannun masu garkuwa da mutanen.

Read also

'Yan bindiga sun sako sarkin Bunguda na Zamfara bayan shafe kwanaki a hannunsu

Daily Trust ta ruwaito cewa, a daren Litinin 'yan bindiga sun kai farmaki makarantar horar da fastoci inda suka tasa keyar dalibai 7 a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.

Kamar yadda shugaban makarantar ya ce:

"Cike da farin ciki, muna daga murya wurin yabo yayin da mu ke sanar da dawowar uku daga cikin dalibanmu da'yan bindiga suka shigo har makaranta suka sace a ranar Litinin 11 ga watan Oktoba.
“Kasa da sa'o'i 48 da sace su, 'yan uwanmu sun samu 'yanci. Muna mika godiya da wadanda suka mana addu'a kan sako su da kuma sauran da ke hannun masu garkuwa da mutanen. Muna fatan Ubangiji ya gaggauta basu 'yanci daga hannun miyagun".
“Ana umartar dukkan limaman mu da su zo shagalin sako su da za a yi a gobe ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba. Muna fatan za a gaggauta sako sauran da ke hannun masu garkuwa da mutanen," yace.

Read also

Sojin sama ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa aikin soja

El-Rufai ya nada babban abokin dan sa matsayin mai gudanarwar 'ƙasar' Kaduna

A wani labari na daban, Muhammad Hafiz Bayero, babban abokin Bello El-Rufai, babban dan gwamnan jihar Kaduna, shi ne Gwamna Nasir El-Rufai ya nada a matsayin mai gudanarwar kasar Kaduna da ya kirkira.

Kasar ta na daya daga cikin ukun da gwamnatin Malam Nasir ta kirkira a cikin makon nan a jihar, Daily Trust ta wallafa.

A yayin sanar da nadin Bayero, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun gwamnan, ya ce majalisar jihar ta amince da dokar kafa hukumomin kula da kasar Kaduna, Kafanchan da Zaria a matsayin birane.

Source: Legit

Online view pixel