Soki burutsu: Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'a yi tashin kiyama

Soki burutsu: Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'a yi tashin kiyama

- Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'a yi tashin kiyama

- Fitaccen masanin kimiyyar nan Isaac Newton ne yayi wannan hasashen

- Yace a shekarar 2060 ne ake sa ran hakan

Masana ilimin kimiyyar sararin samaniya sun gano wasu takardun da suka ce daya daga cikin shahararrun masana fasaha da ilimin kimiyya na duniya da yayi zamani kasar Burtaniya, mai suna Isaac Newton ya rubuta tun a karni na 17 bayan haihuwar Annabi Isah.

Soki burutsu: Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'a yi tashin kiyama
Soki burutsu: Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'a yi tashin kiyama
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Babban buri na idan na lashe zaben 2019 - Buhari

Takardun dai kamar yadda majiyar mu ta TRT Hausa ta bayyana, Masanin kimiyyar Isaac Newton yayi hasashen cewa a shekarar 2060, Annabi Isah zai dawo duniya sannan wata kila ma za a yi tashin kiyama a shekarar.

Legit.ng dai ta samu cewa Mista Newton dake zaman masani wanda ya zo duniya a shekarar 1643, ya yi fice sosai tare da zurfafa bincike kan tsarkakkun litattafai kuma ya fayyace abubuwa da dama musamman ma game da duniyar fasaha da kimiyya.

A takardun da aka gano Newton ya ce: "Tabbas za a yi tashin duniya a shekarar 2060.Amma har yanzu na kasa gano musababbin hakan".

Marubuci Florian Freistetter ya bada cikakken bayanin wannan hasashen na busa kaho da Newton ya yi a littafinsa mai suna: "The As*hole Who Reinvented the Universe", inda ya ce ga dukkan alamu yakin addini, annoba ko kuma wani babban bala'i ne zai rutsa da wannan duniyar.

Idan dai mai karatu bai manta ba haka masanan kimiyyar sukayi ta yin hasashen tashin duniya a shekarar 2000 miladiyya amma hakan bai tabbataba.

Haka zalika kusan dukkan manyan addinan da ake bi a duniya sun yadda da cewa za'a yi tashin duniya, duk da dai cewa ba bu wanda ya san lokacin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng