Bincike: Yawan kananan yara masu teba na karuwa a duniya

Bincike: Yawan kananan yara masu teba na karuwa a duniya

- Bincike ya nuna yawan yara kanana masu kiba na karuwa a duniya

- Yawan kiba kan iya janyo cututtuka a jikin dan Adam

- Yaran da suka taso da kiba sukan zarce har girman su da narkakkiyar teba

A wani bincike da hukumar lafiya ta duniya tayi (WHO), bayan shekara 40 da gudanar da nazarin sun gano cewa kananan yara sun kara teba ninkin-baninkin a kan wadda suke da ita a da. Hakan na nufin kibar yaran ta yi yawa.

Bincike: Yawan kananan yara masu teba na karuwa a duniya
Bincike: Yawan kananan yara masu teba na karuwa a duniya

Yawancin kananan yara da suke tasowa da kiba su kan zarce har girman su ne da narkakiyyar kiba wanda ya kan iya zama lahani a lafiyarsu, ko janyo cututtuka irin su ciwon suga da ciwon daji.

A binciken ya nuna cewa sama da yara da mata milyan 120 ne ke da kibar da ta munana wadda zata iya janyo musu illa a rayuwarsu.

A cikin kasashe 200 ne aka gudanar da binciken wadda aka buga a mujallar Lancet. Daga shekarar 1975 zuwa 2016 an samu adadin yara da suka narka kiba daga miliyan 6 zuwa milyan 74.

DUBA WANNAN: Wata kungiya ta musulmi zata tono gawar mutumin da kwarankwatsa ta fadowa

A yankin Asia ne aka fi samun masu irin tebar, yayin da Amurka kuwa da wasu kasashe na Arewacin Afirka ke rufa mata baya.

Daga hukumar lafiyar ne suke kira ga gwamnatoci da su bullo da wata hanya da zata dau mataki a kan tsayar da samar wa da kananan yara kayan abinci mai dauke da sukari da zai kara musu teba musamman a makarantu da yaran ke zuwa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: