Muna da Kananan Yara 500,000 Da Ba Su Zuwa Makaranta a Kaduna, In Ji Uba Sani

Muna da Kananan Yara 500,000 Da Ba Su Zuwa Makaranta a Kaduna, In Ji Uba Sani

  • Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa adadin yara 500,000 ne ba su zuwa makaranta a Kaduna daga cikin miliyan 14 a faɗin Najeriya
  • Malam Sani ya faɗi haka ne a taron gaddamar da fara ginin sabbin makarantun sakandire 62 a faɗin kananan hukumomi 23
  • Ya ce akwai jihohin da suka fi Kaduna yawan marasa zuwa makaranta amma duk da haka gwamnatinsa ba zata zuba ido ba

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Malam Uba Sani, ya ce daga cikin yara masu gararamba a gari miliyan 14 da ake da su a Najeriya, yara 500,000 'yan jihar Kaduna ne.

Gwamna Sani ya ce duk da wasu jihohin na da irin waɗannan kananan yara da ba su zuwa makaranta fiye da Kaduna, gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen samar da damar neman ilimi musamman ga yara mata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta

Gwamnan Kaduna, Sanata Malam Uba Sani.
Muna da Kananan Yara 500,000 Da Ba Su Zuwa Makaranta a Kaduna, In Ji Uba Sani Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Malam Uba Sani ya bayyana haka ne a wurin taron ɗora tubalin gina sabbin kananan makarantun Sakandire da manyan makarantun Sakandire 62.

Gina sabbin makarantun Sakandiren wani bangare ne na tallafin asusun bankin duniya da ke kula da ilimin 'ya'ya mata (AGILE) a sassan kananan hukumomi 23 na jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taron ya gudana ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta a Nasarawan Rigachikum, ƙaramar hukumar Igabi, kamar yadda gwamna Sani ya wallafa a shafinsa na manhajar X.

A jawabinsa, gwamna Uba Sani ya ce:

"Mun zo nan ne domin ɗora tubalin gina makarantu a Rigachikum, ba don komai ba sai don bai wa kowa damar samun ilimi domin kamar yadda kuka sani Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan yaran da ba su zuwa makaranta a fadin duniya."
“Saboda haka, a yanzu da muke magana, muna da yara miliyan 14 da ba sa zuwa makaranta. A Kaduna muna da kusan 500,000. Jihohi da yawa sun fi jihar Kaduna, amma a Kaduna muna da himma sosai."

Kara karanta wannan

"Za a Ji Daɗi" Babban Abinda Shugaba Tinubu Ya Yi da Kuɗin Tallafin Fetur Ya Bayyana

"Bisa haka ne muke tuntubar dukkan kananan hukumomin domin ganin shirin ya gudana a yankunan karkara saboda ƙananan 'ya'yanmu su samu damar neman ilimi."

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Sani Bello, ya yabawa gwamnan da abokan huldarsa bisa namijin kokarin da suke yi wajen ciyar da ilimi gaba a fadin Kaduna.

Shugaba Tinubu Ya Sauke Jakadan Najeriya A Ƙasar Burtaniya

A wani rahoton kuma Bola Ahned Tinubu ya sauke jakadan Najeriya a ƙasar Burtaniya daga muƙaminsa, ya buƙaci ya tafi hutun kwanaki 60.

A wata sanarwa da ministan harkokin ƙasashen waje ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya gode wa jakadan bisa aikin da ya yi wa ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel