Yadda Juna Biyu Ya Sauya Fasalin Wata Kyakkyawar Mata, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yadda Juna Biyu Ya Sauya Fasalin Wata Kyakkyawar Mata, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata mata yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta saki wani bidiyo na sauyawata da juna biyu ya yi
  • Yayin da take yada bidiyon ban mamakin, matar ta ce tunaninta a kodayaushe shine cewa za ta dunga yanga idan ta samu ciki
  • Sai dai kuma, watanni bayan ta yi ciki, yanayin jiki da kamanninta sun sauya gaba daya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata kyakkyawar mata yar Najeriya ta bai wa mutane mamaki matuka kan yadda ta koma bayan ta samu juna biyu.

Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno gagarumin sauyi a yanayin halittar matar watanni bayan ta samu juna biyu.

Juna biyu ya sauya kamannin wata mata
Yadda Juna Biyu Ya Sauya Fasalin Wata Kyakkyawar Mata, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @lindaikejisblog/Instagram.
Asali: Instagram

Hancinta ya kara girma

Abu na farko da ya fi sauyawa a halitarta shine hancinta wanda ya kara girma ya yi suntum fiye da yadda yake.

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fuskarta ta kara girma lamarin da ya sa wasu mutane mamakin dalilin da yasa ciki ya sauyata da yawa haka.

Jama'a sun yi martani yayin da juna biyu ya sauya wata mata

Yayin da wasu mutane suka nuna shakku kan bidiyon saboda sauyawar mai ban mamaki, bidiyon ya bai wa wasu dariya matuka.

Wasu iyaye mata sun yi amfani da damar wajen bayyana yadda nasu cikin ya kasance da yadda ya sauya su.

Akwenabuoye ya ce:

"Hmmmmm, ku da kuke shakku kan cewa mutum daya ce, ku ci gaba da wasa! Nawa ya fi wannan muni sau 10! Amma mijina ya dunga cewa shi bai lura da kowani sauyi ba a lokacin da nake da ciki, ya ce watakila don yana ganina ne kullun."

Iam_linchpin ta ce:

"Sai da na saka ihu yayin kallon wannan! Mai shirin zama matata don Allah don Allah kuma don Allah kada ki daga mun hankali haka idan kika samu juna biyu."

Kara karanta wannan

Da Gaske Ali Nuhu Yaron Ahmed Musa Ne? Jarumin Ya Fayyace Gaskiyar Lamari

_peaceful_baddie ta ce:

"Sannan wani ebuka zai ce me mata suke yi, kamar da gaske baka san abun da mata ke fuskanta ba a lokacin da suke da ciki."

Kalli bidiyon a kasa:

Rashin miji ya sa budurwa yar shekaru 30 zubar da hawaye

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka cike da dacin rai kan rashin aure yayin da ta kai shekaru 30 a duniya.

A cikin bidiyon da ta yada a shafinta na TikTok, matashiyar ta koka cewa har yanzu babu namijin da ya nemi aurenta a yawan shekaru irin nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel