Kamar Wasa, Wata Mata Ta Koma Yin Rarrafe a Taron Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Kamar Wasa, Wata Mata Ta Koma Yin Rarrafe a Taron Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wata mata tana rarrafe a wajen wani taro ya bayyana a soshiyal kuma ya jefa mutane cikin rudani
  • Lafiyar na tafiyarta lafiya kalau a tsaknin wasu mata biyu kwatsam sai aka ga ta koma yin faffare a kasa
  • Mutane da dama sun yi mamakin muhimmanci ko dalilinta na yin haka, inda wasu suka yi martani a kan tufafin jikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata mata da ke rarrafe a kasa a wajen wani taron biki.

Shafin @cubeyd90 ne ya wallafa bidiyon a TikTok kuma ya jefa masu amfani da intanet cikin rudani yayin da mutane ke neman amsoshi kan abun da ya faru.

Wata mata ta yi rarrafe a wajen taro
Kamar Wasa, Wata Mata Ta Koma Yin Rarrafe a Taron Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @cubeyd90
Asali: TikTok

A cikin bidiyon wanda ya samu mutum miliyan hudu da suka kalle shi, matar ta fara tafiyarta lafiya kalau a tsakanin wasu mata biyu lokacin da ta yi kasa.

Kara karanta wannan

“Ina ta mugayen mafarkai”: Budurwa ta koka bayan ta farke matashin kai da ta siya N800

Cikin yan sakwanni, sai ta fara rarrafe a kasa. Ta rarrafa har sai da ta kai wajen kafar wata da ta fita yawan shekaru wacce ke zaune kan kujera a gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta sumbaci kafar matar sannan sai ta rungume ta. Yayin da suka rungume juna, wata mata ta fito sannan ta fara lika masu kudi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun shiga rudani

S€T£M! ta ce:

"Ba nice amaryar ba nice mai kallon amaryar da tsaki a TikTok."

Fozi ta ce:

"Mahaifiyata na matukar sona da ba za ta bari na yi wannan ba."

Sabira ta ce:

"Yi hakuri ban taba ganin abu mai kama da wannan a al'adarmu ba."

Cee-wai 001 ta ce:

"Matar da ke watsa kudi....menene wannan."

joonhoe ta ce:

"Ina tunanin dole sai ta yi rarrafe sannan ta duka don samun amincewar uwargidar."

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Blinks@official ta ce:

"Idan kan ku ya kulle kamar nawa mu hadu a nan."

Daraunusual ta ce:

"Tana rokon uwar mijin kada ta wargaza mata aurenta cewa soyayya daya ce."

Miji ya je bikon mata da tsire

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo mai ban dariya na sabanin ma'aurata da sulhunsu ya yadu a dandalin soshiyal midiya.

Ya nuna yadda miji ya yi baikon matarsa wacce ta yi yaji bayan sun samu zazzafan sabani a tsakaninsu da tsire.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel