Amarya Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta a Ranar Bikinta

Amarya Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta a Ranar Bikinta

  • Wata kyakkyawar budurwa wacce ta yi kewar mahaifinta a ranar ɗaurin aurenta, ta ziyarci kabarinsa
  • Budurwar ƴar Najeriya ta zubar da ƙwalla lokacin da ta sumbaci kabarin mahaifin na ta yayin da mijinta yake a gefenta
  • Mutanen da suka kalli bidiyon a TikTok sun zubar da ƙwalla saboda ganin amaryar a kabarin mahaifinta

Wata budurwa ƴar Najeriya wacce ta yi kewar rashin mahaifinta, ta ziyarci kabarinsa sanye da rigar amarci domin nuna masa yadda ta yi kewarsa sosai a ranar aurenta.

Budurwar mai amfani da sunan (@detaiyelolu) ta ɗuka a gaban kabarin yayin da mijinta ya riƙe mata hannu, lokacin da take ajiye fulawoyi domin tunawa da mahaifin na ta.

Amarya ta ziyarci kabarin mahaifinta
Amarya ta bayyana cewa ta yi kewar mahaifinta Hoto: @detaiyelolu
Asali: TikTok

Budurwa a rigar amarci ta zauna kan kabari

A cikin bidiyon na ta an nuna lokacin da amaryar ta zauna a saman kabarin domin a ɗauketa hotuna. Ƴan uwanta suna wajen a tare da ita.

Kara karanta wannan

"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Babbar Malamar Addini Ta Fadi Wani Sabon Wahayi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta a cikin bidiyon na TikTok cewa:

"Na yi fatan ace kana nan Baba domin bayar da aurena... Amma na tabbatar cewa ka san lokacin da aka yi bikina."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da ƴan soshiyal midiya suka yi. Ga su nan a ƙasa:

Luckygirl ta rubuta:

"Abun tausayin shi ne ban san mahaifina ba ya rasu, haka ma mahaiifiyata. Ban san yadda son mahaifa yake ba. Allah ya sa sun huta."

Happiness Fyneface ta rubuta

"Allah ya sa ya huta. Kwanan nan zan yi aure nima, amma mahaifina ya rasu."

Adedolapo ya rubuta:

"Omo.. wannan bidiyon ya sanya ni kuka ina tuna yadda mahaifina yake maganar aurena amma yanzu ya rasu. Wannan ne ya sanya ba na son yin aure saboda na san kuka zan yi."

Kara karanta wannan

Malamar Da'awa Ta Fadi Cewa Ta Hango Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

Blackgirl debbie ta rubuta:

"Na san cewa zan yi kuka sosai a ranar aurena, saboda dukkanin iyayena sun rasu."

Budurwa Ta Shanya Saurayinta a Rana Saboda Attajiri

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta shanya saurayinta a tsakar rana saboda zuwa karɓar lambar waya wajen wani attajiri mai mota.

Saurayin na tsaye a rana cikin hakuri yayin da budurwar ta je wurin wani mai mota su na tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel