Dirama Yayin Da Magidanci Ya Kama Garjejen Kato a Dakin Kwanansa

Dirama Yayin Da Magidanci Ya Kama Garjejen Kato a Dakin Kwanansa

  • An samu dirama bayan wani magidanci ya dawo gida ya tarar da wani garjejen ƙato kwance akan gadonsa
  • Magidancin ya tambayi ƙaton da ya kawo masa ziyara gida menene abin da ya kawo shi gidansa ba tare da saninsa ba
  • Garjejejen ƙaton ya koma yin magiya yana neman magidancin ya yi masa rai kada ya ɗauki mummunan mataki a kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyon magidanci yana tambayar wani garjejen ƙaton da ya gani a ɗakin kwanansa ya ɗauki hankula a yanar gizo.

A cikin bidiyon wanda aka sanya a TikTok sannan daga baya aka sanya a X (wanda aka fi sani a baya da Twitter), magidancin ya yi kaciɓus da garjejen ƙaton kwance a daƙin kwanansa.

Magidanci ya kama kato a gadonsa
Magidanci ya yi caraf da garjejen katon akan gadonsa (Hoton an yi amfani da shi ne kawau domin misali) Hoto: Mhlonishwa_Sibalukhulu, Delmaine Donson.
Asali: UGC

Baƙon ƙaton yana kwance akan gadon mutumin inda ya lulluɓe ƙasan jikinsa da mayafi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Kan Gada Cikin Yanayi Mai Ban Tausayi

Magidancin ya titsiye shi da tambayar abin da yake yi a gidansa sannan ya buƙaci ƴar sa Bella da ta zama shaida kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Menene ya kawo ka ɗakin ƙwana na? Me kake yi da matata? Wani ya kira min Bella. A ina ka ke aiki? Ko zan iya ganin katin shaidar ka? Bari na ga ID ɗinka?

Baƙon ya amsa da cewa:

"Bari in ɗauko maka."

Magidanci ya yi faɗa da baƙon da ya kama a kan gadonsa

Magidancin kawai sai ya sauya shawara inda ya buƙaci baƙon da ya cigaba da zama ba sai ya miƙe ba.

"Aa tsaya nan, tsaya nan. Menene kake so a nan? Wannan gida na ne. Ni na gina shi tun daga tushe. Gaya min abin da kake yi a nan?

Baƙon ya buƙaci da ya yi masa rai, inda ya roƙi magidancin kada ya halaka shi.

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Bayan Motar Tirela Ta Murkushe Dan Achaba Da Fasinja a Jihar Kwara

"Abin da yake faruwa shi ne, na ziyarci gidan nan, sannan sai matar nan ta zo...Kada ka kashe ni. Sunana Jerom. Dan Allah kada ka kashe ni. Ni ne namiji babba a wajen mahaifiyata."

Amarya Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta

A wani labarin na daban kuma, Wata budurwa ƴar Najeriya wacce ta yi kewar rashin mahaifinta, ta ziyarci kabarinsa sanye da rigar amarci domin nuna masa yadda ta yi kewarsa sosai a ranar aurenta.

Budurwar ta ɗuka a gaban kabarin yayin da mijinta ya riƙe mata hannu, lokacin da take ajiye fulawoyi domin tunawa da mahaifin na ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel