Babban malamin musulunci Sheikh Alhassan Saeed ya rasu

Babban malamin musulunci Sheikh Alhassan Saeed ya rasu

Allah ya yiwa daya daga cikin manyan malaman kasar nan kuma sakataren kungiyar Ulama, Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Ikamatiss Sunnah (JIBWIS), Sheikh Dr. Alhassan Saeed Adam Jos rasuwa.

Babban malamin musulunci Sheikh Alhassan Saeed ya rasu
Sheikh Alhassan Saeed ya rasu

Legit.ng ta samu labarin cewa malamin ya rasu a Kano, a yammacin yau Laraba, 5 ga watan Afrilu, yana da shekaru 63 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan taRahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Majiya dake kusa da iyalan marigayin sun bayyana cewa malamin ya halarci taron malamai a Jos a ranar Talata sannan kuma ya tafi babban birnin jihar Kano a safiyar yau don ganin likitan sa.

Ya rasu ya bar matayensa da kuma ‘ya’ya da yawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wata yar Arewa da ke gargadin yan Arewa kan shugaba Muhammadu Buhari:

Asali: Legit.ng

Online view pixel