Yadda Marigayi Albani Ya Hango Masifar Janye Tallafin Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Masifar Janye Tallafin Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

  • Muhammad Auwal Adam (Albani) ya taba sukar gwamnatin tarayya kan shirin janye tallafin fetur
  • Malamin musulunci ya ankarar da malamai da sauran ‘yan gwagwarmaya da su yaki wannan tsari
  • Shekaru kusan 10 da yin haka, sai ga Gwamnatin Bola Tinubu ta kawo tsarin da ya tashi farashin fetur

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - A wani fai-fen bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta, an ji yadda Marigayi Muhammad Auwal Adam ya yi maganar cire tallafin fetur.

A wani karatu da ya yi, Legit.ng Hausa ta ci karo da inda Sheikh Muhammad Auwal Adam wanda aka fi sani da Albani Zariya ya fadakar da mutanen Najeriya.

A wancan lokaci, Sheikh Albani Zariya ya ce muddin gwamnatin tarayya ta daina biyan tallafin fetur, za a shiga musibar tsadar da ba a taba gani a tarihi ba.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

Albani Zaria
Auwal Adam Albani Zaria ya soki cire tallafin fetur Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Malamai magada Annabawa

Malamin yake fada shekaru kusan tara da suka wuce cewa sai mutanen kasar sun raina kansu idan aka janye tsarin, ya yi kira da masu fada su tashi-tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albani ya ce ya zama dole ‘yan boko da ‘yan gwagwarmaya su hana cire tallafin da ake mora, ya ce idan ba haka aka yi ba, an gurgunta jama’a da tattalin arziki.

Shehin ya kamanta tashin man fetur da zaluncin shugabannin kasashe irinsu Tanzaniya da Masar, har ta kai ‘yan mata na lalata saboda su samu abinci.

Ana neman ganin bayan 'yan adawa

Babban malamin addinin ya zargi gwamnati da kawo manufar a lokacin saboda karya adawa, a cewarsa mutane na cikin kunci a mulkin Goodluck Jonathan.

A cewar Albani, tsohon Shugaba Ibrahim Babangida ya kawo irin tsare-tsaren domin karbo bashi a hannun manyan Duniya, amma wasu su ka taka masa burki.

Kara karanta wannan

Za a Fi Shan Wahalar Tashin Dala Fiye da Cire Tallafin Fetur da Aka Yi Inji Masani

Mutane za su ji a jika

"Su talakawan kasar ba su san fassarar wannan abin ba, ba su san ma’anar shi ba sai sun ji a jika.
Amma duk ‘dan boko ya san me ake nufi da janye tallafi. Kuma duk Duniya, kowace kasa ta na tallafawa ‘yan kasarta da abin da ke shigowa domin a samu sauki.
Balle abin da arzikinku ne, arzikinku a ce ba za a tallafa maku ba. A lokacin da karuwai ne a yau ake kai wa Neja-Delta, ana yi masu kyautar rijiyar man fetur."

- Muhammad Auwal Adam (Albani)

Mashahurin malamin ya bada misali da malamin jami’a irinsu Shehu Umar, ya ce a yau babu tamkarsa da masu kare hakkin Bil Adama da za su kare al’umma.

Saboda haka wajibi ne ‘Yan Boko ku tashi, ‘yan boko ne su ka tsara abin da ya faru a kasar Masar, Albani ya zaburar da malaman Najeriya su kawo sauyin yanayi.

Kara karanta wannan

Babban Jagora a Kasar Yarabawa Ya Caccaki Tinubu Kan Wahalhalun Da Ake Sha a Najeriya

Za a binciki Abubakar Malami

Dazu aka samu rahoto za a binciki tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami a kan zargin wasu badakala da ake zargin an tafka yana rike da ofishin AGF.

Ana zargin sata ta saci sata a EFCC da wajen karbo dukiyar Janar Sani Abacha, sannan ana tuhumar Malami da biyan lauyoyi da kwararru tulin daloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel