Bidiyon 'Jaye Lo': Farfesa Soyinka Ya Kare Davido, Ya Ce Mawakain Ba Ya Bukatar Neman Afuwar Musulmi

Bidiyon 'Jaye Lo': Farfesa Soyinka Ya Kare Davido, Ya Ce Mawakain Ba Ya Bukatar Neman Afuwar Musulmi

  • Farfesa Wole Soyinka ya kare mawaki Davido kan faifan bidiyon da ya sake da ya jawo cece-kuce a kasar
  • Soyinka ya ce babu bukatar neman afuwa daga wurin Davido inda ya ce yin wakar bai sabawa kowa ba
  • A faifan bidiyon an gano wani yaron Davido, Logos Olori na waka a bakin masallaci yayin da aka hada sallah da rawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa bai kamata Davido ya ba da hakuri akan faifan bidiyon da ya jawo cece-kuce ba musamman a Arewacin Najeriya.

A ranar Juma’a, mawaki Davido ya yada wani faifan bidiyo na wani yaronsa Logos Olori da jama’a ke ganin ya ci zarafin Musulunci, Legit ta tattaro.

Bidiyon Batanci: Farfesa Soyinka Ya Kare Davido, Ya Ce Banda Neman Afuwa
Bidiyon Batanci: Farfesa Soyinka Ya Yi Martani Akan Bidiyon Davido. Hoto: @wolesoyinka, @davido.
Asali: Instagram

Daga bisani, Davido ya ji korafin jama’a inda ya goge faifan bidiyon a ranar Litinin 24 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Soyinka ya ce babu bukatar neman afuwa akan bidiyon

Tribune ta tattaro Soyinka na cewa yin rawa a a gaban masallaci bai sabawa kowa ba a cikin wata sanarwa inda ya ce hakan ba ya bukatar neman afuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ke martani akan kiran da Musulmi ke yi na ya ba da hakuri, musamman daga tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani da Ali Nuhu, Soyinka ya ce:

“Bai kamata ya zama abin mamaki ba idan na ki yarda da yadda aka yada cewa Shehu Sani ya bukaci Davido ya goge bidiyon a madadin Mususlmai.
“Babu bukatar neman afuwa, mu bar bata lokacin mu akan irin wannan lamari, mun san inda ake bukatar neman afuwa da kuma adalci.”

Duk da cewa Soyinka bai kalli faifan bidiyon ba kamar yadda ya ce, ya bayyana cewa rawa a addinance ‘yanci ne na ko wane mawaki ya samu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Davido: Malaman Musulunci Sun Magantu, Sun Fadi Matakin Da Ya Kamata A Dauka

Ya kara da cewa:

“Ban kalli bidiyon ba, amma ina ganin kowa ya na da ‘yancin yin rawa musamman mawaka a addinnance.”

Mutane da dama sun yi martani akan martanin Soyinka:

_leezglam:

“Davido ya gaji yanzu, wani shawara kuma zai bi, ya kamata mutane ku bar shi ya numfasa.”

curtletchristoper:

“Musulmai ba su ta ba neman afuwar kashe Kiristoci ba, ya kamata a wuce wannan wurin.”

joel.oliver:

“Baba ya na cin abinci da kyau ya na barci, kubar damunshi, zai sake wata sabuwar waka kuma za ku saurara.”

Davido Ya Goge Faifan Bidiyon Rashin Da'a Ga Musulunci Da Ake Ta Cece-kuce A Kai

A wani labarin, mawaki Davido ya ji koken mutane tare da goge faifan bidiyon da ya yada a shafinsa na Twitter.

Wannan na zuwa ne bayan mawakin ya yada wani faifan bidiyo da ake ganin cin zarafin Musulunci ne.

A ranar Juma'a ne mawakin ya yada bidiyon inda aka gano wani yaronsa Logos Olori ya hau wakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel