Kyakkyawar Baturiya Ta Kai Saurayinta Ɗan Najeriya Ganin Surukai

Kyakkyawar Baturiya Ta Kai Saurayinta Ɗan Najeriya Ganin Surukai

  • Wata zankaɗeɗiyar baturiya wacce bata san yadda iyayenta za su tarbi saurayin ta ɗan Najeriya ba, tayi ta maza ta kai shi gida
  • Suna isa gidan mahaifan nata, sai iyayen ta suka tarbe shi hannu bibbiyu domin nuna cewa sun yi na'am da shi
  • Ƴan Najeriya da dama waɗanda suka yi tsokaci a kan bidiyon masoyan biyu sun fatan samun irin wannan soyayyar ta su

Wata kyakkyawar baturiya ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da ta kai saurayin ta ɗan Najeriya gida domin ya haɗu da iyayen ta.

Budurwar tace tayi zullumin cewa iyayen ta ba zasu yi maraba da shi ba. Sai dai hakan ba shine abinda ya faru ba domin sun tarbe shi hannu bibbiyu.

Baturiya
Kyakkyawar Baturiya Ta Kai Saurayinta Ɗan Najeriya Ganin Surukai Hoto: TikTok/@samuelandlena
Asali: UGC

A cikin bidiyon an nuna yadda matashin ɗan Najeriya da mahaifiyar budurwar tasa suka buga kwallon kwando tare. Mahaifinta shima ya sakar masa fuska inda suka yi ta ayyuka tare.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Mara Hannuwa Mai Rubutu Da Ƙafarsa Cikin Sauri Ya Ɗauki Hankula Sosai

Mutane da dama waɗanda suka yi tsokaci akan bidiyon, sun yi magana kan yadda soyayyar su ta zama abin ban sha'awa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, sama da mutum ɗari ne suka yi sharhi akan bidiyon, yayin da sama da mutum ɗari biyar suka danna masa alamar 'like'.

Ga kaɗan daga ciki:

LOST BOY ya rubuta:

"Kina da wata ƙaramar ƙanwa.. ko kuma wata ƴar'uwa..?"

John007 ya rubuta:

"Za ki iya kai shi ko ina ne a faɗin duniyar nan, tabbas zai san yadda yayi ya samu ƙauna da yardar mutane."

victor David ya rubuta:

"Wai ni sai yaushe, ina buƙatar abokiyar rayuwa."

Dior ya rubuta:

"Ƴan Najeriya daban suke, sun fi sauran."

France Iv ya rubuta:

"Ta yaya kuka haɗu?"

Ahmed ya rubuta:

"Mahaifinta baya da damuwa."

Kara karanta wannan

Ai Ga Irin Ta Nan: Wasu Ma'aurata Sun Koma Tsilla-Tsilla Bayan Cin Ɗumbin Bashi Da Siyar Da Kadarorin Su Domin Komawa Ƙasar Waje

Wata Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Bayan Ta Gano Sunan Sa Na Ainihi

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta raba gari da saurayinta bayan ta gano wata ƙarya da ya sharara mata.

Budurwar ta koka kan yadda saurayin nata yayi mata ƙaryar sunan sa, wanda sai daga baya taa gano hakan. Tace ba zata iya cigaba da soyayya da shi ba da wannan sunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel