Yadda Wata Mutumiyar Legas tayi Amfani da N200, ta Sace Almajirai a Jihar Borno

Yadda Wata Mutumiyar Legas tayi Amfani da N200, ta Sace Almajirai a Jihar Borno

  • ‘Yan Sanda sun cafke wata Nsa Heneswa da laifin yunkurin sace kananan yara a garin Maiduguri
  • Nsa Heneswa mai shekara 60-69 ta zo Borno ne musamman domin tayi awon gaba da kananan yara
  • Dubun wannan mata ya cika ne a tashar mota bayan har ta dauki almajirai biyu da wata ‘yar yarinya

Borno - Wata Nsa Heneswa, ta shiga hannun dakarun ‘yan sandan Najeriya bisa zargin ta da ake yi da satar wasu kananan yara a Maiduguri, Jihar Borno.

Borno - Daily Trust tace ana zargin wannan dattijuwa mai fiye da shekaru 60 a Duniya ta dauke almajirai biyu da kuma wata karamar yarinyar shekaru 2.

Kwamishinan ‘yan sanda na reshen jihar Borno, Abdu Umar ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da hukumar dillancin labarai na kasa watau NAN a jiya.

Kara karanta wannan

Babban kamu: Mata 7 da ke kai wa Boko Haram kayan abinci sun shiga hannu a Borno

CP Abdu Umar yake cewa an cafke wanda ake zargi ne a tashar motar Borno Express da ke garin Maiduguri tun a ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022.

Nsa Heneswa ta shigo babban birnin na jihar Borno a ranar Laraba, nan take ta wuce kasuwar Monday Market, a nan ne ta ci karo da wadannan 'yan yara.

Kamar yadda jami’in ‘yan sandan ya shaidawa manema labarai, a tashar ta dauke almajiran.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

IGP of Police
Sufetan 'Yan Sanda na kasa, Usman Baba Alkali Hoto: @ngpolice
Asali: Facebook

Ana zargin Nsa Heneswa da satar yara a taha

“Wanda ake zargi ta kira wasu daga cikin yaran, ta ba shi N200. Sai ta bukaci ya biyo ta domin ta saya masa tufafi.”
“Sai ta shiga cikin gari tana kuma neman wani wanda za ta dauke. Sai ta zarce wajen masu fura a unguwar Bulumkutu.
A nan ne ta dauke karamin yaron wata Amina Ayuba, mai saida kindirmo.”

Kara karanta wannan

Miyagun da Sun fi Karfin ‘Yan bindiga Sun bullo, Kila a Hakura da Zabe a yankin Arewa

Kwamishinan ‘dan sandan yace da Heneswa ta zo tasha a ranar, sai ta bukaci motar da ke zuwa Legas, sai ‘yan kamasho suka fada mata mota ta tashi.

Yadda asirinta ya tonu - CP Umar

“Daga nan sai ta nemi a taimaka mata da inda za ta zauna zuwa washegari. Daga nan sai ta sake sace yaro na uku.
Amma asirinta ya tonu da ta dauki yaran su je wurin cin abinci. Daga lura da ita, wani direban Abuja ya fara zarginta.”

Wannan direba ne yayi sanadiyyar da jami’an tsaro suka cafke ta bayan ya tara mata mutane.

Da aka kama ta, tace wannan ne karon ta na farko da tayi wannan danyen aiki. A cewar matar, wata Baiwar Allah ce a Legas ta nuna mata harkar.

An kai Tinubu kara a kotun Abuja

Rahoto ya zo cewa wasu ‘Yan APC sun dauko hayar Lauya, sun yi karar Asiwaju Bola Tinubu bisa zargin yi wa INEC karya a lokacin shiga zaben 1999.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Kwata-kwata babu adalci a Najeriya, dole a sha wahala

Bola Tinubu da APC za su san makomarsu yayin da Alkali ya sa ranar 7 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a saurari shari’arsu a garin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel