Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dakon Kaya Da Sayar Da Soyayyen Nama Na Ke YI: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo

Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dakon Kaya Da Sayar Da Soyayyen Nama Na Ke YI: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya, Dwomoh Emmanuel, wanda ya karanta digiri a bangaren kididdiga ya bayyana yadda rayuwarsa ta canja
  • A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tik-Tok, an hangi matashin dauke da kaya a buhu sannan yana sayar da nama
  • Mutane da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan halin da ya ke ciki suna masa addu'a cewa wata ran zai ga sakayya bisa jajircewarsa

Wani matashi dan Najeriya mai suna Dwomoh Emmanuel, ya tafi TikTok domin nuna sana'ar da ya ke yi akasin abin da ya karanta yayin digiri a jami'a.

Matashin da ya yi digiri a bangaren kididdiga, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana daukan kaya sannan yana sayar da soyayyen kaza a wani shago.

Kara karanta wannan

A cikin ‘yan watanni, ‘Dan shekara 18 ya kirkiri mota mai tafiya kamar ta Bature

Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dako Da Sayar Da Soyayyen Nama: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo
Duk Da Na Yi Digiri Amma Yanzu Dako Da Sayar Da Soyayyen Nama: Matashi Ya Bayyana a Bidiyo. Hoto: Dwomoh Emmanuel.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai digiri ya zama tireda

Mutumin ya dauki babban jaka a kansa. Wani sashi na bidiyon ya nuna shi yana soya wani abu da ya yi kama da fukafukin kaza.

Mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon sun yi addu'ar cewa Allah zai taimake shi ya kai matakin da ya ke so.

Ga bidiyon a kasa:

A lokacin rubuta wannan rahoton, fiye da mutane 1,000 sun tofa albarkacin bakinsu game da bidiyon wasu kuma da dama sun latsa 'like'.

Legit.ng ta tsamo wasu daga cikin abubuwan da mutane suka furta.

Pascalina Matorwmase ta ce:

"Ina fatar wannan bidiyon ya bazu sosai ta yadda za ka hadu da wanda zai taimaka maka."

Lil NAB - GWR ta ce:

"Kai wannan kasar. Allah ya taimake mu baki daya."

Kara karanta wannan

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

Ampem Darko ta ce:

"Bisa hasashe na alkalluma, za ka yi nasara sosai a nan gaba."

Daniell ya ce:

"Bana son in yi dariya amma wannan abin ban dariya ne ... ina mutunta ka dan uwa."

Phinehas Tieku Frimpong ya ce:

"Idan sana'ar mahaifiyarka ne, ka inganta shi zuwa mataki na gaba."

Derek Mani ya ce:

"Mai digiri a bangaren kimiyya yana dakon abincin kaza, ya yi basira."

saheed_hashim ya ce:

"Ko dai mene kowa ya ce, wannan abin yana da ciwo. Ubangiji zai yalwata maka dan uwa. Amin."

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A wani rahoton, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kara karanta wannan

Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel