A cikin ‘yan watanni, ‘Dan shekara 18 ya kirkiri mota mai tafiya kamar ta Bature

A cikin ‘yan watanni, ‘Dan shekara 18 ya kirkiri mota mai tafiya kamar ta Bature

  • Wani mai shekara 18 a Duniya ya kera mota da hannunsa, tun daga farko har motar ta fara tashi
  • Matashin da ya yi wannan abin yabo yana karatunsa ne a wata makaranta da ke Tarkwa a Ghana
  • Bidiyon ya shiga shafin M48 TV a Youtube, yana ta samun yabo da kuma kushen wasu mutanen

Ghana - Wani matashi mai shekara 18 da haihuwa ya nuna irin baiwar da Ubangiji ya yi masa, ta hanyar kikirar wata mota da kansa.

Kamar yadda Legit.ng ta samu ganin wani bidiyo, wannan yaro da yake karatu a makarantar fasaha ya kera motar ne da kansa.

Makarantar da yake karatu ta na wani gari ne mai suna Tarkwa da ke yammacin kasar Ghana.

Bidiyon wannan mota yana shafin M48 TV, kuma a cewar matashin ya yi wannan aiki ne tun daga farko har karshe a watanni takwas.

Kara karanta wannan

Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta

Matashin ya sa wa motar suna ‘Never Give Up’, ma’ana ‘ka da a cire rai’, ganin namijin wahalar da ya sha wajen cin ma burin na sa.

A karshe kuwa, ya yi nasara domin an gan shi yana tukar motarsa ba tare da bada wata matsala ba, motar na kama da kirar nan ta Hilux.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan shekara 18 da ya kirkiri mota
Matashin da ya kera mota Hoto: M48 TV
Asali: UGC

Mutane za su iya ganin wannan bidiyo da kowa yake tofa albarkacin bakinsa a shafin na Youtube.

“Kai! Wannan yaro an yi ‘dan baiwa, yana bukatar a dafa masa.”

- Appiagyei Samuel

Wani ya kushe motar

Shi kuma wani da ya kira kan sa da Lieutenant colonel, kushe motar ya yi, ya ce babu wani abin burgewa da har za a rika magana a kanta.

A ra’ayin Lieutenant colonel, amfani da motar hadari ne ga direbanta domin babu wanda ya san lafiyar injinta, ya bada shawarar a kama shi.

Kara karanta wannan

'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarautar Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno

Colonel yana ganin face-face kurum yaron ya yi, ya fito yana cewa ya kera mota da kan shi.

Za a ga Sir Blay ya maidawa Lieutenant colonel martani, ya nemi jin ko shi ya taba yunkurin kirkirar wani abin da ya kama kafar motar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel