Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

  • Babban kotu a jihar Kano ta umurci Gwamna Abdullahi Ganduje ya biya Ja'afar Ja'afar da Daily Nigerian N800,000
  • Kotun ta ci Ganduje wannan tarar ne bayan da ya janye karar da ya shigar kan Ja'afar na zarginsa da wallafa bidiyon dala da ya ce na bogi ne
  • Lauyoyin Ja'afar da na Daily Nigerian sun kuma nemi kotun ta umurci Ganduje ya biya su N4m sannan ya nemi afuwarsu a wallafa a jaridun kasa

Wata babban kotun jihar Kano, a ranar Talata ta ci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tarar N800,000 bayan ya janye karar bata suna da ya shigar kan mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje ya maka mawallafin Ja'afar Ja'afar a kotu be saboda labari da bidiyon da ya wallafa inda aka gano wani da aka shine ke saka kudaden kasashen waje a cikin aljihunsa.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Daily Trust

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Suleiman Danmallan, wadda ta amince da dakatar da shari'ar, ta umurci gwamnan ya biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa na jaridar N400,000 kowannensu.

Abubuwan da lauyoyin Ja'afar Ja'afar da New Nigerian suka nema

Lauyoyin da suke kare wadanda aka yi kararsu, Ubi Eteng da Muhammad Danazumi sun bukaci kotun ta biya su miliyan 400 a matsayin kudin dakatar da shari'ar amma lauyan Ganduje O.E.B. Offiong (SAN) ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar, yana mai cewa a bar wannan batun zuwa gaba tunda wanda aka yi karar shima ya shigar da wata kara.

A karar da Ja'afar ya shigar kamar yadda Daily Trust ta gani, mawallafin ya bukaci kotun ta ayyana cewa karar da gwamnan ya shigar 'bata da nagarta, babu hujja, ya shigar ne domin neman kudi tare da neman huce fushi.'

Ya kuma bukaci kotun ta ayyana cewa 'amfani da aka yi da yan daba, jiga-jigan yan siyasa da dalibai frimari a harabar majalisar dokokin jihar Kano inda suke rika zaginsa bai dace ba, rashin mutunci ne da rashin sanin ya kamata.'

KU KARANTA: 'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

Hakan yasa ya bukaci kotun ta umurci gwamnan ya nemi afwarsa ba hanyar wallafawa a manyan jaridun kasa a kalla guda biyu kan shigar da kara mara hujja a kansa.

Kazalika, ya bukaci kotun ta saka dokar hana gwamnan, mukarrabansa da kowanne mutum sake shigar da shi (Ja'afar) kara a kan wannan lamarin bidiyon dala.

Amma, alkalin ya ce za a sake saka sabuwar rana domin sauraron bukatar bangarorin biyu

Majalisar jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji

Rahoton da BBC ta wallafa na cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji Rimin Gado, shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa na jihar na tsawon wata daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa dakatarwar na Muhyi na zuwa ne sakamakon kin amincewa da ya yi da akawun da aka aika masa daga ofishin babban akawun jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan korafin da ofishin babban akawun jihar ya shigar ne a gaban majalisar dokokin jihar a kan Muhyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel