Latest
Muƙaddashin shugabam PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa zaben da tsagin Wike suka shirya na shugabannin jam'iyya a Kudu maso Kudu ya saɓa doka.
Sabon rahoto ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara ne ya kafa rundunar Lakurawa a 1997 domin yaki da masu satar shanu.
Majalisa ta yabawa ƙoƙarin rundunar sojoji inda kwamitin kudi ya gabatar da wani muhimmin kuduri don cire harajin kudin shiga na dakarun duba da yanayin ayyukansu.
SanataBarau Jibrin ya karbi shugabannin 'yan Arewa a Legas zuwa APC bayan sauya sheka. Za a kafa tafiyar Arewa domin marawa Sanata Barau baya da cigaba.
Ministan sadarwa, Mohammed Idris ya ce sauye-sauyen da ake yi suna haifar da sakamako mai kyau, yana mai yabawa hakurin ‘yan Najeriya da kira ga kara addu’o’i.
Majalisar dattawan Najeriya ta kada kuri'ar amincewa da shugabancin Sanata Godswill Akpabio. Majalisar ta nuna cewa ta gamsu da kamun ludayin shugabancin Akpabio.
Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna na nuna cewa mahara sun tashi mutanen garuruwa 5, sun sace wasu matasa a rugar fulani.
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta zuba ido a rika amfani da tashe ana tayar da hankula a jihar ba, kuma tuni kwamitin tsaron da aka kafa ya fara hana karya doka.
Bayan samun gawar wata ƴar TikTok da ke zama a Kenya, Kamfanin Teleperformance ya musanta zargin hana matashiyar, Ladi Olubunmi, izinin zuwa hutunta a gida.
Masu zafi
Samu kari