Latest
Rundunar sojin Najeriya ta ware kwanaki uku domin zaman makoki da jimami kan zaratan sojoji 17 da aka kashe a jihar Neja. An ware kwanakin ne don girmama su
Jam'iyyar APC ta tabbatar da murabus din Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam'iyyar. APC ta yi wa Ganduje fatan alheri bayan kammala shugabancin jam'iyya.
Dubun wasu matasa ya cika bayan da jami'an tsaron majalisar tarayya sun damke su saboda zargin satar manya wayoyin lantarki masu tsadar gaske a Abuja.
Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu bayan Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga kujerar shugabancin APC, lamarim dai ya zo ba zato ba tsammani yau Juma'a.
Wani bam da ake zargin 'yan ta'adda ne suka dasa shi ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a jihar Yobe. Wasu mutane kuma sun jikkata sakamakon fashewar.
Yayin da aka kwashe kwana 12 ana gwabza fada, shugaban Amurka Donald Trump ya fadi yadda ya kare rayuwar jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei na Iran.
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin APC, mataimakin shugaban APC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa, Alhaji Bukar Dalori, shi ne zai maye gurbin Abdullahi Ganduje.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ismael Ahmed a matsayin shugaban PCNGi domin rage wa ‘yan kasa raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi a farkon mulkinsa.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya buɗe sabon ofishin NNPP na Abuja ana tsaka da batun murabus din Ganduje.
Masu zafi
Samu kari