Latest
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa an yi wa matakin da suka dauka kan tura sakamakon zabe ta na'ura gurguwar fahimta.
Tsohon Ministan sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Farfesa Ali Isa Pantami ya sabunta rajistar zama dan APC. Ya ce Buhari ya ba shi shawara.
Bayanai daga mazauna yankunan da yan bindiga suka kai hari a Kwara na nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya tunkari 100, an ce an tura jami'an tsaro.
A labarin nan, za a ji cewa Solomom Dalung, tsohon Minista a gwamnatin baya ya zargi gwamnati da nuna wariya da ta kai Abubalar Malami da dansa kotu.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da dokar zabe. Majalisar dattawan ta kuma cimma matsaya kan kudirin neman tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Yayin da ake ta surutu kan rashin kamma'a gyara a dokar zaben Najeriya, Majalisar dattawa ta amince da kudin garambawul a dokar domin inganta harkokin zabe.
Sanatocin Taraba, Haruna Manu da Shuaibu Isa Lau, sun fice daga PDP zuwa APC yau 4 ga Fabrairu, 2026. APC ta mamaye majalisa da kujeru 81 yayin da PDP ke durƙushewa.
Wani dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Muhammad Basil, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ja baya da siyasa.
Shugaban karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, Sirajo Daudawa ya tabbatar da cewa an rasa akalla mutane 20 a harin da yan bindiga suka kai garin Doma.
Masu zafi
Samu kari