Latest
Nasir El-Rufai zai dawo Nijeriya nan da sa'o'i 48 domin amsa kiran EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026. Ya musanta zargin tserewa zuwa waje don gujewa masu bincike.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito fili ya caccaki gwamnatin shugaba Donald Trump game da saka bakin da ya yi a Najeriya ya harzuka 'yan majalisar Amurka.
A labarin nan, za a ji cewa fitaccen ɗan jarida Jaafar Jaafar da wasu kiristocin Najeriya sun yi martani a kan zargin da su Riley Moore ke yinwa Kwankwaso.
Erdogan ya naɗa Akin Gurlek a matsayin Ministan Shari'a, matakin da ya janyo dambe a majalisar Turkiyya da kuma fushin jam'iyyar adawa a ranar 11 ga Fabrairu, 2026.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta jaddada cewa sojoji ne za su ci gaba da yanke duk wani aiki da za a iya ko da kuwa sojojin Amurka sun shigo kasar nan.
Kungiyar Fulani Makiyaya ta MACBAN ta yi wa Amurka martani kan neman saka mata takunkumi bisa zargin keta hakkin addini. Sun ce su ba 'yan ta'adda ba ne.
A labarin nan, za a ji cewa Isyaku AbdusSamad Khalifa Rabiu ya samu babban matsayi a harkokin gudanar yau da kullum da kamfanin BUA da ke jihar Legas.
Mutum 2 sun tsira bayan ƙaramin jirgi ya faɗa kan motoci a Georgia. Matuƙin ya yi ban kwana da iyalinsa kafin sauƙar gaggawa a ranar 9 ga Fabrairu, 2026.
Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin 'yan majalisar Amurka na neman saka wa Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi. Ta ce bata yarda ba a tauye masa hakki ba.
Masu zafi
Samu kari