
Latest







Wasu yan bindiga sun tare wani jigon jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom sun harbe shi har lahira jim kaɗan bayan ya halarci taron addu'a na sabuwar shekara a coci.

Wani mummunan hari da 'yan bindiga suka sake kai wa a Kaduna yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, tare da sace wasu masu yawa yankin Kerewa a jihar Kaduna.

Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, yace zai yi shawara kafin ya yanke hukunci kan tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023.

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da mata da kuma ɗan kanin kwamishinan muhalli na jihar Enugu, Chijioke Edeoga, da daren ranar Asabar.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace idan jam'iyyar PDP ta dake kurkuren watsi da kiran yan Najeriya a wannan lokacin to zai wahala Allah ya gafarta mata.

Wata masarauta a Arewacin Najeriya ta nada wata shararriyar jarumar fina-finai a Najeriya a matsayin sarauniya a ata masarauta a jihar Nasarawa. Ga hotuna.

Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna. Ya ce zai kaca-kaca da jam'iyyar APC da 'yan takararta.

Lamurra biyu, mutuwa da biki a jihar Kano sun sauya lissafin siyasa na jihar Kan kafin zuwan zaben 2023, wanda hakan yasa masu kiyasi ke kallon ketowar alfijir.

Wasu tsagerun yan bindiga sun sace wani babban jigon jam'iyyar PDP reshen jihar Filato, Nkemi Nicholas Nshe, a gidansa dake yankin karamar hukumar Shendam.
Masu zafi
Samu kari