Bola Tinubu: Najeriya na matukar bukatar na mulke ta saboda wasu dalilai da ke kasa

Bola Tinubu: Najeriya na matukar bukatar na mulke ta saboda wasu dalilai da ke kasa

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya gana da shugabannin majalisun dokokin jihohin APC
  • Tinubu ya yi wannan ganawa da jiga-jigan 'yan siyasa ne a jihar Legas, kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Tinubu ya yi jawabi, ya ce shi ne Najeriya ke bukata domin kawo ci gaba ta fuskoki masu yawan gaske

Jihar Legas - Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo kudaden shiga da gina kasa kamarsa.

Ya bayyana kansa a matsayin mutumin da Najeriya ke bukata a tafiyar ta zuwa garin harkokin ci gaba.

Tinubu yayi magana ne a wajen taron kwana daya tsakanin shuwagabannin majalisar wakilai da mataimakansu na Jihohin da APC ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Sai da nemi kujerar gwamna sau 4 kafin na yi nasara a 1999, Atiku Abubakar

Tinubu na gwada kansa
Dan takarar shugaba kasa Tinubu: 'Yan Najeriya na matukar bukatar na mulke su | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Taken tarin shi ne ‘Majalisar Dokoki, Canje-canjen Zamani da Tafiyar Dimokuradiyyar Najeriya’.

Kakakin majalisar dokokin Legas Mudashiru Obasa ne ya karbi bakuncinsa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya ce:

“Najeriya na bukata ta kamar yadda nake bukatar Najeriya. Najeriya na bukatar tsattsauran sauye-sauye masu kyau da za su kawo kudaden shiga kuma ni ne mai jajircewar da take bukata."

Hakazalika, Tinubu ya siffanta kansa a matsayin mutumin da ya gina rayuwarsa akan jajircewa, don haka Najeriya ke bukatar mutum irinsa.

Ya kara da cewa:

"Hanzarta ciyar da al'ummarmu gaba batu ne na tunani da aiki, kuma a shirye nake in sake yin hakan saboda ni mai tunani ne kuma mai aikatawa."

Ya kuma roki ‘yan majalisar da suka ziyarce shi da kada su tsaya su kadai, su tsaya tsayin daka, su hada kai, su zama daya, domin aikin mayar da Najeriya wacce ta ke kasa daya, kamar yadda The Guardian ta ruwiato.

Kara karanta wannan

Jerin rukunin mutane 4 da ke takaicin bayyanar burin Osinbajo na gaje Buhari

Martanin shugabannin majalisa

Shugaban taron, kuma kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana cewa ‘yan majalisar dokokin jihar na da matukar muhimmanci a harkokin dimokuradiyya a matsayin wadanda suka fi kowa kusanci da jama’a.

Suleiman ya bayyana Tinubu a matsayin babban jigo mai hali da sadaukarwa, wanda ke ba da fifiko ga jin dadin ‘yan jam’iyyarsa.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya godewa shugabannin majalisun da mataimakansu bisa amsa gayata.

Sanwo-Olu ya ce Tinubu na da abin da ake bukata don yiwa Najeriya abubuwa da yawa na ci gaba.

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

A wani labarin, a ranar Laraba, 13 ga wata ne, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8, Shehu Sani, ya ce shi dai ya jinin siyasa ubangida.

Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga jawabin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Osinbajo dai shi ne dan takarar shugaban kasan da ya fito karara daga cikin 'yan takarar APC ya ce zai dora mulkinsa daga inda shugaba Buhari ya tsaya, lamarin da bai yiwa 'yan kasar da dama dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel