Jihohin Arewa su ne a gaba yayin da aka kashe mutane 2, 968 a cikin watanni 3 a 2022

Jihohin Arewa su ne a gaba yayin da aka kashe mutane 2, 968 a cikin watanni 3 a 2022

  • Tsakanin Junairu zuwa watan Maris na shekarar bana, an kashe Bayin Allah kusan 3000 a Najeriya
  • Alkaluman da Nigeria Security Tracker ta fitar ya nuna cewa an kuma yi garkuwa da mutum 1400
  • Jihohin da suka fi fuskantar wannan matsala sun hada da Neja, Kaduna, Zamfara duk a yankin Arewa

Nigeria - Akalla mutane 2, 968 aka kashe daga watan Junairu zuwa Maris a shekarar nan ta 2022. Haka zalika an yi garkuwa da mutane 1, 484 a kasar nan.

Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Laraba, alkaluman da Nigeria Security Tracker (NST) suka fitar a makon nan ya tabbatar da haka.

Nigeria Security Tracker su kan tattara bayanai a game da rayukan da aka rasa a Duniya. Sannan su na tara alkaluma a kan garkuwa da mutane da ake yi.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa Sanatocin Kebbi, Jigawa da Taraba da suka yi gaba da kudin talakawa

NST ta tabbatar da cewa ana fama da miyagun ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa. A Kudu, Sojojin ESN na IPOB ne suka fitina jama’a.

Tsagerun Neja-Delta su kan yi ta’adi a jihohi irinsu Ribas, Kuros Riba da Akwa Ibom har gobe. A kudu maso yamma ana kukan ‘yan fashi da kungiyoyin asiri.

Adadin rayukan da aka rasa

Alkaluman sun bayyana cewa a yankin Arewa maso yamma ne aka fi fama da kashe-kashe. A cikin watanni ukun farko na bana, an kashe mutum har 1, 103.

Dakarun tsaro
Hafsoshin sojoji na kasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yankin Arewa maso tsakiya ne ya zo na biyu a wannan lokaci da mutuwar mutum 984. Sannan a shiyyar Arewa maso gabas an yi rashin akalla mutum 488.

Daga Junairu zuwa Maris, an rasa rayuka 181 a Kudu maso gabas. A wannan sa’ili ne aka kashe mutane 127 da 85 a Kudu maso yamma da kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

Har Da Kano: Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku

Mutane 2000 sun mutu a jihohi 5

A takaice dai an hallaka mutane 2, 575 (fiye da 85%) daga bangaren Arewacin Najeriya. A gefe guda kuma, a yankin Kudu an kashe mutane 393 (kusan 15%).

Jihohin da lamarin rashin tsaro ya fi kamari su ne Neja (840), Zamfara (404), Borno (392), Kaduna (332), sai Kebbi (114). A jihohin biyar, an rasa rayuka 2, 082.

Garkuwa da mutane a 2022

A watannin nan uku kuma an yi garkuwa da mutane 1, 354 a yankin Arewa (91%). Jaridar ta ce ana da labarin satar mutane 130 a Kudancin Najeriya (9%).

Mutum 623 aka dauke a watan Junairu, a watan Fubrairu aka sace 342, sai aka samu 519 a Maris. Abin ya fi yawa ne a Neja, Kaduna, Zamfara, Katsina da Kogi.

Tsageru su na jawowa kasa asara

Kwanaki aka ji labari shugaban kamfanin mai na kasa na NNPC, Mele Kolo Kyari ya koka a game da yadda masu fasa bututun mai ke cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Bayan haka ana fama da matatun da ke satar danyen mai a Kudu. Wannan matsala ta jawo ana maganar gwamnatin tarayya ta yi asarar $1.5bn a shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel