Sabon hari: ‘Yan bindiga sun tare motar matafiya, sun sace direba da matafiya 8

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun tare motar matafiya, sun sace direba da matafiya 8

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare motar fasinja, sun sace direba da fasinjojinsa a jihar Ribas ta kudancin kasar nan
  • Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga
  • Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna ci gaba da bincike

Jihar Ribas - Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata motar bas mai dauke da fasinjoji takwas da ke tafiya a kan titin Buguma/Degema/Abonema da ke kan titin East-West a Jihar Ribas.

Wata majiya ta ce maharan sun tare motar bas din ne da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Litinin inda suka tafi da direban motar da dukkan fasinjojinsa zuwa wani wuri.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu

Majiyar ta ce an kai wa motar bas hari ne a kusa da Kasuwar Ahiankwo da ke kan hanyar Emohua zuwa Kalabari yayin da ta nufi yankin kogi daga Fatakwal.

Yadda 'yan bindiga suka sace mutane a kudu
Sabon hari: ‘Yan bindiga sun tare motar matafiya, sun sace direba da matafiya 8 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Depositphotos

Har yanzu ba a san inda direban bas din da matafiyan suke ba, kana maharan ba su tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin 'yan sanda

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana kokarin kubutar da fasinjojin tare da damke wadanda suka yi garkuwa da su.

Ta ce:

“Eh, muna sane da lamarin, kuma ana ci gaba da bincike. Wata motar bas kirar Opel ce aka kai wa harin inda aka yi garkuwa da fasinjoji takwas.
"Mun tattara jami'anmu na dabaru don tabbatar da cewa an kubutar da wadanda aka sace ba tare da wani rauni ba, tare da kama masu garkuwa da mutanen."

Kara karanta wannan

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani, suka sace 'yarsa mai shekaru 15 a Zaria

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Dorayi da ke unguwar Dutsen Abba a karamar hukumar Zaria, inda suka kashe wani Alhaji Abdullahi Ardo tare da sace ‘yarsa mai shekaru 15 mai suna Mariya.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 2 na safe, inda suka tafi kai tsaye gidan marigayin, inji rahoton Daily Trust.

Wani ganau ya ce:

“Daga nan ne suka tafi ba tare da kai hari a kan wani gida ko mutum ba. Muna jin sun zo ne musamman don daukar Alhaji Ardo, da suka yi yunkurin haka, watakila ya yi turjiya, shi ya sa suka harbe shi, sannan suka yi awon gaba da ‘yarsa.”

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

A wani labarin, 'yan bindiga sun kutsa wani yanki na garin Tsafe kuma sun sace dalibai biyar na kwalejin kiwon lafiya da fasaha da ke tsafe a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Laraba. Wata majiya ta sanar da cewa miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai ne suka dira gidan daliban wanda yake wajen makaranta.

Ya ce 'yan bindiga ba za su taba samun damar shiga makarantar ba saboda jami'an tsaron da ke kofar shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel