A shekara daya zan dawo da komai dai-dai a Najeirya, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

A shekara daya zan dawo da komai dai-dai a Najeirya, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya lashi takobin kawo sauyi a Najeriya cikin shekara ɗaya da zaran yan Najeriya sun ba shi dama
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ya ce idan bai gyara Najeriya a wannan lokacin ba a masa kiranye
  • Ya yi wannan furucin ne a Sakatariyar PDP ta ƙasa yayin da ya je maida Fam ɗin nuna sha'awar takara

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ya roki shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa su ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe.

Anyim ya ɗau alƙawarin dawo da sa'ar Najeriya, komai ya koma dai-dai cikin shekara ɗaya bayan ya ɗare mulki, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim.
A shekara daya zan dawo da komai dai-dai a Najeirya, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023 Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Tsohon shugaban Sanatocin ya yi wannan rokon ne jim kaɗan bayan maida Fam din sha'awar takara a Sakatariyar PDP ta ƙasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC da Sanata sun sanar da Buhari zasu shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Ya kuma ƙara da cewa kwarewar da ya tara lokacin da yake kan mulki ya kai shi matsayin da zai iya lallasa kowa ya samu nasara a zaɓe don cigaban PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me ya sa a gaba game da takarar da yake?

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin ayyuka (NWC) na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Anyim ya shaida musu cewa zai kafa gwamnati mai inganci da zaran sun ba shi damar da yake so.

Gwamnati wacce zata canza akalar ƙasar nan zuwa hanyar zaman lafiya, cigaba mai dorewa da kwanciyar hankali, inji ɗan takaran.

A kalamansa ya ce:

"Mai girma shugaban jam'iyya, idan har shekara ɗaya ta cika bayan na zama shugaban ƙasa, yan Najeriya ba su ga canji da banbanci tsakanin duhu da haske ba, ku mun kiranye."

A wani labarin na daban kuma Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Kara karanta wannan

2023: Bayan samun ƙarin mutum biyu, yan takarar dake hangen kujerar Buhari a PDP sun kai 15

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun maida martani kan wasu hotunan kafin Aure na yar Najeriya da ya watsu

Ba tantama hakan na da alaƙa da gajartar mutumin idan aka kwatanta da girman jikin kyakkyawar budurwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel