Hotuna da jerin sunayen sabbin kwamishinonin NPC da ICPC da Shugaba Buhari ya rantsar da su

Hotuna da jerin sunayen sabbin kwamishinonin NPC da ICPC da Shugaba Buhari ya rantsar da su

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamisinonin hukumomin kididdiga ta kasa (NPC) da na yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC
  • An rantsar da kwamishinonin ne a wani dan takaitaccen biki da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Jim kadan bayan nan, shugaban kasar ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na mako a yau Laraba, 13 ga watan Afrilu

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar kididdiga ta kasa (NPC) da na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar a kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa ta Twitter, an gudanar da dan takaitaccen taro na rantsarwar ne jim kadan kafin fara zaman majalisar zartarwa.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

An rantsar da sabbin kwamishinonin a zauren majalisar zartarwar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.

Hotuna da jerin sunayen sabbin kwamishinonin NPC da ICPC da Shugaba Buhari ya rantsar da su
Hotuna da jerin sunayen sabbin kwamishinonin NPC da ICPC da Shugaba Buhari ya rantsar da su Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Sunayen kwamishinonin na NPC da aka rantsar bayan majalisar dattawa ta tabbatar da su a watan da ya gabata sune:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Cif Benedict Ukpong Effiong (Akwa Ibom)

2. Misis Gloria Fateya Izonfo (Bayelsa)

3. Kupchi Patricia Ori Iyanya (Benue)

4. Dr. Haliru Bala (Kebbi)

5. Dr. Eyitayo Oyekunle Oyetunji (Oyo)

Kwamishinonin ICPC da Buhari ya rantsar sune:

1. AIG Olugbenga Adeyanju, mai ritaya (Ekiti)

2. Sanata Anthony Agbo (Ebonyi)

3. Anne Otelafu Odey (Cross River)

4. Alhaji Goni Ali Gujba (Yobe)

5. Dr Louis Solomon Mandama (Adamawa)

Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa

A halin da ake ciki, shugaban kasar na jagorantar zaman majalisar zartawa na mako.

Wadanda suka halarci zaman sune mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin da suka gana da Tinubu a Abuja bayan bayyanar burin Osinbajo

Ministocin da suka hallara sune Atoni janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami; takwaransa na labarai da al’adu, Lai Mohammed; na kwadago, Chris Ngige; na noma, Mahmud Abubakar; na muhalli, Mohammed Abdullahi; na lantarki, Abubakar Aliyu.

Sauran sune ministar kudi, Zainab Ahmed; na albarkatun ruwa, Suleiman Adamu; na kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu da karamin ministan lafiya, Olorunimbe Mammora.

Sauran ministocin da shugabar ma’aikatan tarayya, Folasade Yemi-Esan, suna bin taron ne ta yanar gizo daga ofishoshinsu.

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

A wani labarin, gwamnan jihar Bauchi kuma mai aniyar son zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bala Mohammed ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake magana a daren ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, a wajen wani taro da tsoffin ministocin gwamnatin PDP suka shirya, Mohammed ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta lalata komai da komai na kasar, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel