Katin gayyata 20 muka buga, mun samu 500k, Amarya da angon da suka yi karamin biki

Katin gayyata 20 muka buga, mun samu 500k, Amarya da angon da suka yi karamin biki

  • Wani 'dan Najeriya, Ademola Adebusoye wanda ya yi dan kwarya-kwaryar shagalin biki ya shawarci masu shirin aure da su yi abunda za su iya
  • Dan kasuwa kuma hazikin manajan ya labartawa Legit.ng yadda ya gabatar da kwarya-kwaryar shagalin bikinsa da masoyiyarsa, Titilope Adebusoye
  • A cewar Ademola, sun buga katikan biki 20, amma sun samu kusan N500,000 bayan an gama lika musu kudi a wurin rawa

Bayan kauda kai daga kashe-kashen kudi da tada kurar da aka san yawancin 'yan Najeriya nayi a shagulgulan bikinsu, wasu ma'aurata sun yanke shawarar yin aure ta hanyar hada karamin liyafa.

Ademola Adebusoye da masoyiyarsa, Titilope Adebusoye, sun yi aure a 2020 a Legas, sannan ya bayyana farin cikinsa na yadda suka yi dan kwarya-kwaryar shagali, inda ya shawarci masoya a wata wallafa da ya yi cikin kwanakin nan da sun yi abunda zasu iya.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

Katin gayyata 20 muka buga, mun samu 500k, Amarya da angon da suka yi karamin biki
Katin gayyata 20 muka buga, mun samu 500k, Amarya da angon da suka yi karamin biki. Hoto daga @iamthatgeorge
Asali: Twitter

Ademola ya bayyana yadda suka yi dan kwarya-kwaryar shagalin biki yayin tattaunawa da Legit.ng, inda Ademola ya ce lokacin sun yi niyyar yin aure, amma basu da kudin daukar ragamar bikin.

A cewarsa, da a ce sun so, da sun yi bikin kece raini duk da basu da isashshen kudi - Saboda su biyun duka suna aiki a lokacin - amma ba yaso su kashe duk kudadensu a bikin.

"Saboda haka a lokacin mun shirya yin aure, amma bamu da isashshen kudi a hannunmu. Duk da ina samun kudi domin ina da aikin yi - ita ma tana aiki.
"Ta so a yi shagali sosai, duk ba wai can babba ba amma yafi wanda na kawo shawara.
"Saboda haka dole na dauki ragamar wasu abubuwan irinsu rigunan da zata sa a ranar bikin - aka yi su yadda take so," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada

Abunda da yafi komai tsada a bikinsu shi ne dakin taron da suka kama, wanda ya fi komai ja musu kudi a bikin, fasihin manajan ya ce dakin shagalin ya kai kusan N300,000.

Haka zalika, don tabbatar da ra'ayinsu na yin kwarya-kwaryar shagalin biki, sun buga katika 20 amma kusan mutane 200 sun halarci bikin.

"Ba muyi auren majami'a ba. Auren kotu muka yi a ranar Alhamis, sannan muka sa rana da shagalin biki a ranar Asabar. Mun samu kusan baki 200 ( iyayen mata ta suka yi fotokwafin katikan gayyatar (ya yi dariya)."

Ademola ya labarta yadda suka yi nadama a kan bikin, yayin da aka tambaye shi ko sun yi nadama a kan taron da suka gabatar, Ademola ya ce, abunda kawai muka yi dana-sani shi ne yadda bamu tsaya a kan katika 20 da muka buga ba.

A cewarsa: "Babu abunda da muka yi dana-sanin yi. Maganar gaskiya mun so a ce mun tsaya a kan katikan da muka buga kadai, da ta haka ne ya kamata mu nemi wani dakin taron da bai kai wannan girma ba da kwararan mutanen da muka yi niyya.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

"Ba mu ga kashi 98 cikin dari na mutanen da suka zo bikin kafin taron ba, sannan ba mu gansu ba ko bayan an kare taron."

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin.

A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.

Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng