Rashin Tsaro: Ra'ayin Shehu Sani Ya Banbanta Da Na Dattawan Arewa, Ya Ce A Ƙyalle Buhari Ya Kammala Wa'adinsa

Rashin Tsaro: Ra'ayin Shehu Sani Ya Banbanta Da Na Dattawan Arewa, Ya Ce A Ƙyalle Buhari Ya Kammala Wa'adinsa

  • Tsohon sanata, Shehu Sani ya nuna rashin amincewarsa da kudirin Kungiyar Dattawan Arewa, NEF na batun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga karagar mulki saboda rashin tsaro
  • An samu bayanai akan yadda a ranar Laraba NEF ta bukaci shugaba Buhari ya yi murabus saboda yadda ya gaza samar da mafita ga matsalar tsaron kasar nan
  • Kungiyar ta bayyana bukatarta ne ta kakakinta, Dr Hakeem Baba-Ahmed inda ta ce shekaru 7 kenan da Buhari yake kan madafun iko amma ya kasa kawo garanbawul ga matsalar tsaro

Shehu Sani, tsohon sanata ya bayyana rashin amincewarsa da bukatar Kungiyar Dattawan Arewa, NEF akan cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda gazawa akan tsaron Najeriya.

The Punch ta ruwaito cewa ranar Talata NEF ta nemi Buhari ya sauka daga kujerarsa akan kasa samar da tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu

Ku Kyalle Buhari Ya Kammala Wa’adinsa, Shehu Sani Ga Dattawan Arewa
Ku Bar Buhari Ya Kammala Wa’adinsa, Shehu Sani Ya Fada wa Dattawan Arewa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Kakakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana bukatar kungiyar inda ya ce abin kunya ne ace shekaru 7 Buhari yana kan kujerar shugaban kasa amma ya kasa kawo tsaro ga kasar nan.

Baba-Ahmed ya bayyana abinda kundin tsarin mulki ya tanadar

Kamar yadda Baba-Ahmed ya ce kuma The Punch ta ruwaito:

“Mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kasa kawo karshen matsalar tsaron kasar nan wanda ya dade da bayyana karara.
“Ba za mu iya ci gaba da zama karkashin makasa, masu garkuwa da mutane, masu fyade da mugayen ‘yan ta’adda kuma muntuwa saboda su ba. An kasa ba mu hakkinmu na zaman lafiya da tsaro.
“Kundin tsarin mulkinmu ya samar da gabar da shugaba zai yi murabus dakanshi akan wani dalili ko kuma yana ganin ba zai iya shugabanci ba.”

Kara karanta wannan

Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

Sani ya nuna rashin amincewarsa ne ta wata wallafa da ya yi a Twitter

Sai dai a ranar Laraba, Sani wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8 ya bukaci NEF ta bar Buhari ya kammala mulkinsa.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya ce a bar shi ya kammala mulkinsa don ya samu damar shirya zabe a shekarar 2023.

Kamar yadda ya wallafa:

“Dattawanmu na Arewa masu daraja suna so Buhari ya sauka daga mulki; ni kuma a bangarena sai nake ganin hakan ba daidai bane. A bar Baba ya gama mulkinsa kuma ya shirya zabe da kanshi.”

Har Da Kano: Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku

A wani rahoton, Buhari ya amince da bude Kwalejojin Fasaha (Polytechnic) guda uku na tarayya a bangarori daban-daban na kasar nan a matsayin hanyar saukaka wa jama’a damar samun ilimin gaba da sakandare.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

A wata takarda wacce Darektan watsa labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Mr Ben Bem Goong ya saki a ranar Talata a Abuja ya shaida hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel