Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gonar Gidan Yari, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Sace Dabobbi Masu Yawa
- ‘Yan bindiga sun afka gonar Gidan Gyaran Hali da ke garin Kujama, hedkwatar karamar hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna
- Sakamakon farmakin da suka kai da safiyar Litinin kamar yadda majiyoyi suka bayyana sun halaka mutum daya sannan sun sace shanu da dama
- Wani shugaba a Kujama wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya kazanta
Kaduna - 'Yan bindiga sun kai hari wani gidan gona da ke Gidan Gyaran Hali a garin Kujama, hedkwatar karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna inda suka halaka mutum daya da shanu masu yawa.
Sun sace dabbobi da dama sakamakon harin kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har yanzu dai babu wanda zai iya bayyana asalin abinda ya faru amma ‘yan bindiga sun isa gonar a ranar Litinin da safe kamar yadda majiyoyin yankin suka tabbatar.
City and Crime ta gano cewa ‘yan bindigan sun je gonar ne kai tsaye inda suka sace shanu da wasu dabbobi.
Wani shugaba a Kujama wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya bayar da tsoro, rahoton LIB.
Har yanzu ba a bayyana sunan wanda suka halaka
A cewarsa:
“Eh, ‘yan bindiga sun kai hari gonar da safiyar Litinin inda suka sace shanu da tumakin Gidan Gyaran halin. Sun halaka mutum daya a cikin gonar.”
Wakilin Daily Trust bai tabbatar da sunan mutumin da suka halaka ba a gonar.
Yayin da aka tuntubi Shugaban Hukumar Gidan Gyaran Hali na Jihar, Umar Audu, ya tura wakilin Daily Trust zuwa hedkwatarsu da ke Abuja inda ta ce sun tura duk wasu bayanai can.
'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama
A wani labarin, ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.
An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.
Asali: Legit.ng