Dausayin Ramadana: Abubuwa 17 da suka hallata ga mai azumi, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadana: Abubuwa 17 da suka hallata ga mai azumi, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan jerin abubuwa 17 ga Musulmi mai azumi watan Ramadana.

Akwai abubuwa masu yawa da suka halatta mai azumi ya yi su.

1. Ya halatta mai azumi ya kurkure bakinsa, zai iya shaka ruwa, amma sai dai kada ya kai matuka wajen kurkurar ko shakar, saboda gudun kada ruwan ya sulluɓe ya shige maƙogwaro.

Saboda hadisin Laƙiɗu Ɗan Sabirah RA inda yake cewa, na tambayi Manzon Allah ﷺ game da alwala? Sai Ma’aiki ﷺ ya ce,

“Ka cika alwala kuma tsetstsefe tsakanin ‘yan yatsu, kuma ka kai matuƙa wajen shaka ruwa, sai dai in azumi kake yi.” (84)

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe Fitaccen ɗan kasuwa har Lahira a gaban Budurwar da zai Aura mako mai zuwa

2. Mutum zai iya yin wanka domin ya ji sanyi a jikinsa, wato ya halatta ga mai azumi ya zuba ruwa a kansa, ko ya yi wanka saboda tsananin zafin da yake ji a jikinsa, ko kuma saboda ƙishirwa da ta dame shi, don yaji ɗan sanyi-sanyi.

An ruwaito hadisin wani daga cikin sahabban Ma’aiki ﷺ yana cewa, na ga Manzon Allah ﷺ a wani wuri yana zuba ruwa a kansa saboda tsananin ƙishi ko saboda tsananin zafi.” (85)

3. Babu laifi mai azumi ya shafa mai, man sanyi ko na zafi, a duk gaɓoɓin jikinsa har da leb e da hanci, ma’ana mai azumi zai iya shafa man sanyi a lebe, wato kamar (rob) ko (mentholatum) da makamantan, ko ya shafa a cikin hanci da rana ko da daddare duka wannan babu laifi.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Ko da Mun Yi Saɓani, Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Saboda shafa mai na kwalliya ko na magani ba ya karya azumi. Kamar yadda sheikh Jibrin ya ba da fatawa a kai.

4. Amfani da aswaki, ya halatta mai azumi ya yi amfani da aswaki a kodayaushe ya so yin hakan, duk da cewa hadisi ya zo Manzon Allah ﷺ ya ce,

“Warin bakin mai azumi ya fi ƙamshi a wajen Allah ﷻ Fiye da turaren almiski.”

Duk da haka wannan ba ya hana mai azumi ya goge bakinsa da aswaki ko duk wani abin goge baki da Shari'a ta amince da shi.

Sai dai idan zai goge bakin nasa da man goge baki na bature ya tabbatar ya kurkure bakinsa in ya gama. Idan kuwa aswakin ne, sai ya riƙa yi yana furzar da furtacin aswakin daga bakinsa don kada ya haɗiye.

5. Haɗiye abin da ba za a iya kiyaye shi ba, kamar yawu, domin mai azumi ya halatta ya haɗiye yawun bakinsa kamar yadda muka ambata a baya.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Haka nan babu laifi ga mai aikin ƙasa idan kurar ƙasar da yake aiki ta shiga bakinsa ya haɗiye ta, tare da yawun bakinsa babu laifi, ko masu aikin nika gari, ko makanikai masu gyaran mota ko babur, idan hayaƙin da yake fita ta salansar ababan gyaran ya shiga bakinsu babu komai ko da zai yi kaki ya ga baƙi-baƙin hayaƙin a majinarsa azuminsa bai ɓaci ba.

6. Haka nan ƙamshin miya, man shanu, kori, wainar ƙwai, ƙamshin dakan fura ko ƙamshin turare duka waɗannan ba sa karya azumi. Haka nan idan majina ko kaki suka wuce makogwaro ba zato ba tsammani azumi bai karye ba.

Haka nan mai azumi zai iya shafa turare ko ya fesa shi a jikinsa ko a tufafinsa yin hakan babu komai, sai dai wasu malami sun ce idan turaren hayaƙi ne, wato turaren wuta ko na tsinke an so mai azumi ya ɗan yi nesa da shi.

Kara karanta wannan

Na shirya tsayawa gaban Allah ranar Lahira kan kalaman da na faɗa, Sheikh Khalid

Saboda za a iya shaƙarsa ya taru a ciki, ka ga ya zamo kamar an zuba abinci ne a cikin, sai dai fa a sani cewa shaƙar turaren wuta ko na tsinke ba haramun ba ne. Sai dai kawai an so mai azumi ya yi nesa da shi kaɗan.

7. Sa kwalli, domin nana A’ishah ( RA) ta ce, Manzon Allah ﷺ ya sa kwalli alhali yana azumi. (86)

8. Yin ƙaho, ma’anar ƙaho shi ne a tsaga jiki ko fata domin a fitar da mataccen jinni kamar yadda wanzamai suke yi, idan mutum ya yi ƙaho alhali yana azumi da rana wannan bai karya masa azumi ba, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Abbas (RA) wanda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya yi ƙaho alhali yana azumi.”

Akwai hadisinnsa ya ce mai ƙaho da wanda aka yiwa ƙaho duk azumin su ya karye wannan mansuk ne ma'ana an dakatar da aiki da shi.

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

9. Danɗana abinci ga mai azumi shi ma ba ya karya azumi. Haka nan ma taunawa. Misali, za a ba yaro ko tsoho wani abu mai tauri, to babu laifi mai azumi ya tattauna musu a bakinsa, sai ya fito da shi ya kurkure bakinsa, babu komai matuƙar dai bai haɗiye wani abu daga abin da ya tauna ɗin ba.

Haka kuma ɗanɗana abinci domin a ji gishiri ya ji, ko maggi, ko sikari, ko kuma tsamiyar ta isa, wannan duka babu komai. Kamar dai yadda aka ruwaito halaccin hakan daga Abdullahi Ɗan Abbas (RA) kamar yadda bayani ya gabata a baya.

10. Yin allura, malamai da dama sun ba da fatawar halaccin yin allura ga mai azumi da sharaɗin kasancewar ta ba ta abinci ba ce. Ma'ana ba allurar da ake yinta ne a matsayin abinci ba.

11. Haka nan irin abin shaƙawa ɗinnan da masu ciwon asma suke shaƙa shi a baki, shi ma ba ya karya azumi domin malamai sun ce yana bin hanyoyin iska ne, bawai yana zuwa uwar hanji ba ne, don haka idan mai ciwon asma ya shaƙa wannan maganin a bakinsa bai karya masa azuminsa ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu

12. Amfani da maganin da zai jinkirta zuwan haila ko ya ɗauke ta shi ma ba laifi. Ma’ana idan mace ta sha wani magani don hailarta ta ɗauke domin ta sami damar iya yin azumi, ko kuma ta sha maganin domin hana jinin zuwa saboda ta sami damar yin azuminta gaba ɗaya, wannan babu laifi, domin sashin fuƙaha’u na wannan zamanin sun ba da fatawar halaccin mace ta sha wani abin da zai ɗauke mata jinin hailarta, ko ya jinkirta zuwansa har na tsawon kwanakin watan Ramadhan, matuƙar dai ta yi shawara da likita ya ce, shan maganin ba zai cutar da ita ba, ko ya shafi tsarin al’adarta, domin ta sami damar yin azuminta da sallolinta tare da mutane cikin kwanciyar hankali. (89)

13. Mutum zai iya saduwa da matarsa da daddare bayan an sha ruwa daga nan har zuwa lokacin da alfijir na biyu zai bayyana. Sai dai kawai ya yi ƙoƙari ya tabbatar rana ta faɗi a lokacin da zai sadu da su ɗin, kuma ya tabbatar alfijir bai fito ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi

Amma da za a ce alfijir yana fitowa da ƙarfe biyar (5), sai shi kuma ya ci abincin sahur ɗinsa da ƙarfe huɗu da rabi, bayan ya gama kuma sai ya sadu da iyalinsa zuwa ƙarfe biyar saura kwata, shike nan babu laifi domin dai alfijir bai fito ba, kuma ba a hana yin jima’i don an yi sahur ba, matuƙar dai ba alfijir ne ya fito ba, amma idan ya bari alfijir ya fito azzakarinsa yana cikin farjin matarsa, wannan yana iya karya masa azumi.

14. Babu laifi don mutum ya wayi gari da janaba, misali, mutum ya sadu da matarsa sai bacci ya ɗauke shi bai yi wanka ba har sai da gari ya waye, sai kawai ya je ya yi wanka azuminsa yana nan sai ya ci gaba da shi ba za a ce azuminsa ya karye don ya wayi gari da janaba a jikinsa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i ya yi gaskiya, hanya ɗaya ce ta kawo karshen yan ta'adda, Tinubu ya magantu

15. Idan mutum ya yi mafarki da rana, wato mutum ne ya yi bacci da rana a watan Ramadhan sai ya yi mafarkin yana saduwa da mace, da ya farka sai ya ga ruwan maniyyi ya zubo masa to wannan bai karya masa azuminsa ba, sai kawai ya ci gaba da azuminsa, haka ne ita ma mace. Ingancin azumin wanda ya wayi gari da janaba a watan Ramadhan azuminsa bai karye ba, shi ne hadisin Nana A’ishah da Ummu Salama inda suke cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana wayar gari da janaba ta saduwa da iyalinsa, sannan sai ya je ya yi wanka ya ci gaba da azuminsa.” (90)

16. Babu laifi idan mai azumi ya taba jikin matarsa da rana ko ya sumbance ta, ko kuma ya rungume ta da rana matuƙar dai ya san cewa, wannan rungumar ko taɓa jikin ko sumbantar ba za ta iya sabbaba masa karyewar azumin ba, babu laifi

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

amma idan ya san hakan zai iya afkuwa, to an hana shi aikatawa, domin Ummina A’ishah ta ce, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sumbantar iyalinsa da rana a watan azumi amma fa shi ya fi ku tsare kansa da kuma mallakar sha’awarsa.” (91) A wani hadisin kuma Nana A’ishah tana cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sumbanta ta alhalin shi yana azumi ni ma ina azumi.” (92)

17- mai haila da mai nifasi, idan jini ya ɗauke musu da daddare to babu laifi su yi wanka su ci gaba da azuminsu idan kuma mace ta ɗauki azumi da daddare da gari yawaye rana ta yi sai ta ga jinin al’adarta ya zo, to wannan azumin ya ɓaci, sai kawai ta ci gaba da cin abincinta, bayan sallah sai ta rama shi. Haka nan kuma idan jininta ya ɗauke da rana to shi ma za ta ci gaba da cin abincinta ne har faɗuwar rana ba za a ce ta kame bakinta a ragowar wunin ba. Allah ﷻ shi ne masani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel