Latest
Yayin da ake zargin tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya koma gida da daddare, Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan ƴan sanda ya kama shi nan take.
Tsohon kwamishina a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa ana ta shirye-shiryen raka sarki Aminu Ado Bayero fadarsa dake kofar kudu.
Rahotannin da. ke fitowa sun nuna cewa yanzu haka jami'an tsaro sun mamaye wurare masu muhimmanci a gidan gwamnatin jihar Kano, ba su hana shige da fice ba.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya isa fadarsa da ke birnin inda ya ke maraba da dandazon Kanawa da suka zo fadar domin tarbarsa duk da halin da ake ciki yanzu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta a ciki a baya. Ya yi alkawari yi aiki tukuru.
Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa yanzu haka daraktan DSS da wasu manyan shugabannin hukumomin tsaro a Kani sun koma cikin fadar da Sanusi yake.
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ya bayyana cewa har yanzu suna bin umarnin kotu da ta hana gwamnatin Kano nada sabon sarki.
Yayin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai shiga fada, matasa daga kowane ɓangare sun cika harabar yayin da Aminu Ado ya shigo jihar Kano a yau Asabar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ga zargi mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da hannu a rikicin masarautar Kano.
Masu zafi
Samu kari