Latest
Kungiyar kwadago NLC ta fitar da sanarwa da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni kan ci gaba da yajin aiki inda ta ce sai an ji daga gare ta kan matakin da za ta dauka
Shahararraiyar kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana takaici kan yadda yajin aikinNLC zai shafi musulmin Najeriya yayin jigilarsu.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya magantu kan halin da ya shiga a gidan yari da ke Yola inda ya ce marigayi Lamidon Adamawa ya taimake shi a zamansa.
Yayin da ake tururuwa zuwa fadar Muhammadu Sanusi II, ƴaƴan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun ziyarci fadar Sarkin tare da nuna goyon baya da addu'o'i gare shi.
Kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa AHOUN ta bukaci kungiyoyin NLC da TUC sun dakatar da yajin aiki saboda kaucewa taba addini da jawo wa mahajjata asara.
Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya ce suna shirin jawo tsofaffin mambobin jam'iyyar domin su dawo gida ciki har da Peter Obi Obi.
Rahotanni sun bayyana cewa wakilan gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun kamma zaman da aka kira na gaggawa kan yajin aiki a ofishin SGf George Akume.
Yajin aikin da ƴan kwadago suka fara yau ya hana zaman sauraron ƙara game da rikicin masarautar Kano ranar Litinin, an ɗage zaman shari'ar har sai baba ta gani.
Kungiyar ma'aikatan kotu reshen birnin tarayya Abuja sun rufe manyan kotuna tare da hana alkalai, lauyoyi da masu shigar da kara aiki saboda yajin aikin NLC.
Masu zafi
Samu kari