Latest
Ɗan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Ifelodun/Boripe da Boluwaduro a jihar Osun, Soji Adetunji ya gwangwaje ƴan mazaɓarsa bayan harin da matasa suka kai masa.
Senegal ta shiga sahun kasashe masu arzikin man fetur bayan da kamfanin Woodside Energy na Australiya ya sanar da fara aikin hakar man a kasar da ke yammacin Afirka.
Iyalan Shehin Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ibrahim Nyass sun buƙaci Muhammadu Sanusi II ya hakura da sarauta Kano, ya yi kori da kakansa Muhammadu Sanusi I.
Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sayo sababbin jiragen sama domin amfanin shugaban kasa da mataimakin sa.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da kyautar Naira miliyan 6 ga iyalan ‘yan sanda hudu tare da wasu jami’an tsaro uku na jihar wadanda ‘yan bindiga suka kashe su.
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bayyana samun nasara kan wasu miyagu da ke taimakawa ‘yan ta’adda su na muzgunawa al’umaar kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.
Sojojin Najeriya sun kai tagwayen farmaki kan 'yan ta'adda a jihohin Abia da Ondo a kudancin Najeriya. Farmakin ya jawo lalata sansanin 'yan ta'addan IPOB da ESAN.
Aliko Dangote ya bayyana cewa kungiyoyin masu aikata laifuffuka na cikin gida da na waje sun yi yunkurin yin zagon kasa a aikin matatar man da ya gina a Legas.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta haram dukkanin bangarori biyu da ke rikicin masarautar Kano gudanar da hawan Sallah a babbar Sallah da ke tafe.
Masu zafi
Samu kari